Aisha Usman Adam ficacciyar Jarumar Kannywood ce Content Creator, Model, ‘Yar Kasuwa, kuma Mai Tallata Kayayyaki.
Aisha Usman Adam, ta yi fice a matsayin ɗaya daga cikin fitattun jaruman Hausa na kafafen sada zumunta bayan ta samu karɓuwa ta hanyar gajerun bidiyoyin TikTok, musamman shirin Amaryar TikTok.
Inda ta fito tare da Mohammad Adam Idris da sauran masu shirya fina-finan Hausa na yanar gizo.
A wannan ranar, ita da Mohammad Adam Idris sun yi hira ta musamman da BBC Hausa.
Inda suka bayyana cewa manufar shirin ita ce nishaɗantar da al’umma tare da isar da saƙonni masu amfani da tarbiyya.
Tun daga wannan lokaci, Aysha ta ci gaba da faɗaɗa sunanta a matsayin jaruma, model, content creator, kuma ‘yar kasuwa.
Tana amfani da TikTok, Instagram da sauran kafafen sada zumunta wajen gabatar da fina-finai, tallace-tallacen kayayyaki da haɗin gwiwa da kamfanoni.
Ta kuma samu karramawa a matsayin Jakadiyar Wayar da Kan Jama’a kan Cutar Hawan Jini (Hypertension Ambassador) saboda gudummawar da take bayarwa wajen wayar da kan jama’a.
Daga 2024–2026: Ta ci gaba da kasancewa cikin fitattun masu content creators na Hausa, tana fitowa a sababbin shirye-shiryen TikTok, halartar tarukan nishaɗi, da kuma ƙara yawan mabiya a shafukanta na TikTok da Instagram.
A yau, Aysha Usman Adam tana daga cikin matasan jaruman Kannywood da suka yi tasiri sosai a duniyar nishaɗin dijital.
Inda ake kallonta a matsayin ɗaya daga cikin taurarin TikTok da suka taimaka wajen bunƙasa masana’antar nishaɗin Hausa ta yan






