Home Rahoto Yan bindiga sun kashe mutane 6 tare da jikkata mutane 5 a...

Yan bindiga sun kashe mutane 6 tare da jikkata mutane 5 a sabon hari a jihar Sokoto

25
0

Yan bindiga ne sun kashe mutum shida tare da jikkata biyar a wani sabon hari da suka kai ƙauyen Lajinge da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

Daily Trust ta rawaito cewa rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 12:00 na dare zuwa kusan ƙarfe 2:20 na safe, inda su ka riƙa harbe-harbe ba tare da ƙa’ida ba, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici.

Baya ga kashe mutanen, maharan sun kuma yi awon gaba da dabbobi masu yawa kafin daga bisani su tsere.

Wani mazaunin yankin ya ce daga cikin waɗanda aka kashe akwai wata matar aure, yayin da waɗanda suka jikkata ke samun kulawa a asibiti.

An riga an yi jana’izar waɗanda suka rasu bisa koyarwar addinin Musulunci.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar Sokoto da wakilan yankin ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here