Home Labarai Ƙudirin gayyatar Tinubu ya haifar da hatsaniya a Majalisar Waƙilan Nijeriya

Ƙudirin gayyatar Tinubu ya haifar da hatsaniya a Majalisar Waƙilan Nijeriya

35
0

An samu hayaniya a zaman Majalisar wakilai ta tarayya a ranar Laraba bayan da ‘yan majalisar suka samu sabani kan wani kudiri da ke neman a gayyaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya yi bayani kan jinkirin aiwatar da kasafin kudin shekarar 2025.

A yayin zaman, dan majalisar mai wakiltar mazabar Okpe/Sapele/Uvwie ta jihar Delta, Benedict Etanabene, ya tayar da batun gaggawa inda ya jawo hankalin majalisar kan wata takarda da Akanta Janar na Tarayya, Shamseldeen Ogunjimi, ya fitar a ranar 29 ga Yuni.

A cikin takardar, Ogunjimi ya umarci dukkan ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya da su dakatar da biyan kudaden ayyukan mazabu da na shiyyoyi (Zonal Intervention Projects) har sai Ma’aikatar Ayyuka na Musamman da Hulɗar Gwamnatoci ta tantance su tare da amincewa da su.

Etanabene ya ce wannan mataki na iya kara jinkirta aiwatar da kasafin kudin 2025, saboda haka ya bukaci majalisar ta gayyaci Shugaba Tinubu domin ya yi wa ‘yan majalisar bayani kan dalilan jinkirin aiwatar da kasafin.

Bukatar tasa ta haifar da muhawara mai zafi a zauren majalisar, lamarin da ya rikide zuwa hayaniya yayin da ‘yan majalisar suka kasa cimma matsaya kan kudirin. Ana sa ran karin bayani kan lamarin zai biyo baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here