Home Hausa Films Tsohuwar matar Adam Zango ta faɗi dalilin rabuwar Arensu

Tsohuwar matar Adam Zango ta faɗi dalilin rabuwar Arensu

20
0

Tsohuwar matar Jarumi Adam A. Zango Jaruma Maimuna Musa Pretty ta ce, zancen gaskiya ba batun gwajin jini ne ya yi sanadin mutuwar aurenta da Adamu Zango ba.

Maimuna ta shaida wa Arewa Updates cewa, sun goyi bayan abin da ya faɗa na gwajin jini ita da mahaifiyarta don a rufe bakin mutane daga lamarin.

Ta jaddada cewa tun kafin su yi aure sun yi gwaji kuma suka nemi shawarwarin likitoci.

Ta ce, auren ya mutu ne sakamakon abubuwa daga dangi da masu sharrance-sharrance da aka nemi ƙala mata.

Maimuna ta ƙara da cewam ita kanta mahaifiyarta da ta kare shi mutane sai da suka bi ta da sharri suna cewa wai ita ta tilasta sai an yi saki.

Ta ƙara da cewa, wasu na ta yaɗa ƙarerayi ciki har da cewa wai ta je Saudiyya tana yi wa mahaifiyar Adamu Zango adduʼar Allah ya sa ta rasu, wasu sun ce, wai ta ce sai ta musguna wa ƴarsa Murjanatu, wasu kuma suka ce ma wai maza take bi.

Amma ta ce, duk waɗannan manyan sharruka da aka yi mata ta bar wa Allah ya yi mata sakayya.

Kazalika, Maimuna ta jaddada cewa, ta yi duk mai yiwuwa da bin duk wata hanya don ganin an samu daidaito kar aurensu ya mutu amma abin bai yiwu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here