Home Siyasa Tsaro mutanen Sakkwato ke buƙata ba tallafin shinkafa ba – Ɗan takarar...

Tsaro mutanen Sakkwato ke buƙata ba tallafin shinkafa ba – Ɗan takarar gwamna na NDC ga Gwamnan Sakkwato 

18
0

Ɗan takarar gwamnan jihar Sakkwato na jam’iyyar NDC, Dokta Shamsudden Aliyu Haido, ya buƙaci gwamnatin jihar ta mayar da hankali kan magance matsalar tsaro, yana mai cewa abin da al’umma ke buƙata shi ne kariya daga hare-haren ‘yan bindiga, ba tallafin shinkafa da kuɗi kawai ba.

Dokta Haido ya bayyana hakan ne bayan ziyarar da Mataimakin Gwamnan Sakkwato ya kai wa mutanen da hare-haren ‘yan bindiga suka raba da muhallansu a yankin Dan Gulbi da wasu ƙauyuka da ke ƙaramar hukumar Tureta.

Ɗan takarar NDC ya nuna damuwarsa kan matsalar tsaro da ta ƙara ƙaimi a jihar Sakkwato musamman a karkara in da mutane ke ta fuskantar matsin rayuwa da muhalli.

A cewar Haido tallafin jinƙai kamar shinkafa da kuɗi suna rage raɗaɗi na wuccin gadi ne ga waɗanda lamarin ya shafa, abin da yakamata a samar na dindin bai wuce tsaro ba mutane su koma gidajensu cikin aminci.

“Mutanen Sakkwato suna buƙatar tsaro fiye da kuɗi da buhunana shinkafa, mutane nason  kariya su yi barci idanunsu a rufe, su tafi gona ba wani fargaba, su tafi duk in da suke ba wata damuwa,” a cewarsa.

Dakta Haido ya fahimci mutanen da ke gudun hijira a wasu yankunan jiha na buƙatar ɗaukin gaggawa kan tsaro a kuma ɗauki matakan hana yaɗuwar aiyukkan ‘yan bindiga.

Ya koka kan matsin rayuwa da ‘yan gudun hijira ke fuskanta da yawansu sun rasa muhalli, gona da dabobi da wasu abubuwan gudanar da rayuwa kan hare-haren kullum. In suka cigaba da dogara da kayan tallafi ba zai taɓa magance ƙalubalen da suka shafi garuruwan su ba.

Ɗan takarar gwamnan ya nemi gwamnati ta ƙarfafa haɗin kai da shugabanni da jami’an tsaro da ƙungiyoyi a ƙananan hukumomi don samun bayanan sirri da za su taimaka wurin tsare rayukkan talakawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here