Home Manyan Labaru Maganin Basir yake Mana—-Masu yin Akurkura

Maganin Basir yake Mana—-Masu yin Akurkura

16
0

Akurkura wani kayan shaye-shaye ne da yake bugar da mutane da aka samu matasa da tsofaffi maza sun duƙufa wajen sansa domin maganin Basir.

Kafin hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta sanya dokar hana sha da sayar da shi ana sayarwa a shagunan maganin musulunci ko a kan titin Bauchi ko a titin Ahmadu Bello ko a unguwar Difiloma a birnin jihar Sakkwato.

Abin shan a yanzu ya zama haɗari a cikin mutane ganin yanda tsofaffi a cikin al’umma ke nemansa domin sha saɓanin sauran kayan maye da aka barwa matasa kaɗai.

Wani da yake shan Akurkura ya yi wa wakilinmu bayanin cewa “Ni ina shan a Akurkura ne domin maganin Basir bai taɓa bugar dani ba, duk na kurƙua zuwa wani ɗan lokaci zan shiga toilet na yi kashi baƙi cikina ya wanke na ji ƙarfin jikina, haka nake yi lokaci-lokaci, wani sirrinsa kana qara kurkurarsa kana qara jin qarfin jikinka.

“Marfin kwalbar nake cikawa sai na Kurkura wani zubin ina haɗewa amma ba ko yaushe ba, yanzu an daina samunsa a fili amma dai mun san in da ake samu, yanzu ana sayar da kwalba Naira 1000 saɓanin baya da  bai yi wuyar samu ba,” a cewarsa.

Ba ka ganin tana da matsala ga lafiyar ka? ya ce “ban ganin haka domin ni lafiya take bani na faɗa maka duk na sha zan ji ƙarfi a jikina Basir da ke damuna ya ragewa  sosai, in dai ina samu zan ci gaba da sha gaskiya, kuma dai har yanzu dai ina samu ba ta gagara ba.”

Wani da ya fara ya bari ya ce wani lokaci ne abokinsa yake gaya masa in yana son maganin basir ya Kurkura zai yi masa, haka aka yi da ya yi yafi awa ɗaya bai san mi yake yi ba, ya ga ƙasa yana juyawa da shi, a haka aka ɗaura shi saman babur ya tafi gida daga lokacin bai ƙara yi ba.

Wani kuma ya ce abokinsa ne yake yi kullum, shi kuma taba ce da ake shaƙawa yake shaƙa sai ya yanke shawarar zai yi Akurkura ya gani, ko zai yi masa maganin basir da ake faxa “na saye na tafi gida na cire tufafi, na zauna a ɗaki na, na kurkura, nake gaya maka daga nan sai na ji wani tsam tun daga kan farce na babba har zuwa ƙwaƙwalwata na daɗe kwance na kasa komai tun a lokacin na cigaba da shaƙe na ban sake yin Akurkura ba.”

Ya ce nafahimci ana sanya mata taba gari hakan ya sa take bugar da mutane, wasu za su yi bai bugar da su ba, wasu kuma za su ta bugar da su, har hauka wasu ke yi kanta.

Yana ganin da wahala a daina yinta domin a gida ake samar da ita duk yanda hukuma ta yi ba za ta iya hanawa ba tun da ba shigowa ake yi da ita ba daga waje anan Nijeriya ake samar da ita, tun da ka har yanzu masu yi ba su daina samunta ba, duk da ana kama masu sayar da ita.

Bala Gadanga jami’in kiyon lafiya ne a Sakkwato da yakai matakin darakta ne jami’ar kimiya da fasaha ta SAISA a jihar ya ce “waton Akurkara ko Kuskure ko Akuskura dukkan ana faxi ne da Hausa wani nau’i ne na Guba akwai na ruwansa da gari wanda yake mutane suna amfani da shi, wannan Akurkura haxe-hade ne na Guba da ake haxa wasu gayen na gargajiya da ganyen taba da ganyen tabar Wiwi da sauran wasu ganye masu guba a haka ake samar da wannan sinadaren na na Akuskura.

“Saboda haka ne hukumar NDLEA ta haramta wannan magani da ake kira Kuskure domin haxarin da yake da shi, yana haifar da mtsalar qwaqwalwa ka riqa jin sautin magana ba in da ake yinta ba, yana canja tunanin mutum ka riqa yin mummunan tunani yana sanya jigjiga(karkarwa), yana sanya saurin motsi daga jikin xan adam akai-akai, yana sanya tashin hankali mutum ya kasa nutsuwa, yana sanya tsinkewar fatar mutum, yana sanya canja hankali duk wani abuu da ba ya da kyau sai ka ganshi mai kyau ne, yana sanya ganin jiri ya ga gari na juyawa, yana sanya gyambon ciki waton Ulcer, in mutum ya daxe yana shan sha zai iya tava masa Anta ko Qodarsa, defenders zai kama wanda ke shansa ya zama bai iya komai sai ya sha shi, matsalolinsa suna da yawan gaske yakamata mutane su guje shi domin a zauna lafiya,” Kalaman Bala Gadanga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here