Sokoto ta koma tarkon mutuwa
Wasu ɓangarori a jihar Sakkwato sun koma matattarar ‘yan bindiga, a kwanan nan a ƙalla sun kashe magidanta 15 an yi garkuwa da sama da mutum 79 a ƙananan hukumomi shidda a jihar Sakkwato.
Hare-haren bayan nan a Raɓah da Dange shuni da Isa da Boɗinga da Keɓɓe da Goronyo da Tureta da Tambuwal da wasu yankunan a ƙananan hukumomin jihar ya haifar da damuwa yanda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara.






