Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun kama wani da ake zargi da kai wa ’yan ta’adda kuɗaɗe da kayayyaki, inda suka samu Naira miliyan 5.302 a hannunsa a jihar Zamfara.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an gudanar da samamen ne ranar 7 ga Agusta, inda dakarun suka kuma lalata wata na’urar fashewa ta IED da aka dasa a kan babbar hanya kusa da ƙauyen Jabanda da ke ƙaramar hukumar Zurmi.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce dakarun sashe na 2 sun gano na’urar tare da tawagar ’yan sandan da ke kula da abubuwan fashewa, sannan suka share hanyar tare da tabbatar da cewa ba wata matsala ga masu zirga-zirga.
Ya ce dakarun sun kuma yi arangama da ’yan ta’adda a ƙananan hukumomin Birnin Magaji da Shinkafi, inda suka tilasta musu tserewa zuwa cikin daji. Daga baya an gano babura, kayan sojoji da na’urar sadarwa.






