Home Labarai ‘Yan bindiga sun yi ajalin jami’an tsaro biyu da ɗan ƙasar waje...

‘Yan bindiga sun yi ajalin jami’an tsaro biyu da ɗan ƙasar waje ɗaya a harin Kebbi

4
0

Barayin daji sun yi ajalin jami’an tsaro biyu da ɗan ƙasar waje a harin Kebbi

Rahoton gidan talabijin na Channels ya ce aƙalla mutane uku sun mutu, ciki har da jami’an tsaro biyu da wani ɗan ƙasar waje da ke aiki a aikin gina babbar hanyar Sokoto-Badagry, bayan da wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne suka kai hari wurin aikin a ƙauyen Gubba da ke ƙaramar hukumar Maiyama ta jihar Kebbi.

Rahoton ya ce an dakatar da aikin ginin hanyar na ɗan lokaci yayin da jami’an tsaro ke ƙara sa ido da matakan kare ma’aikata.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Bashir Usman, ya ce wasu fararen hula biyu sun jikkata, yayin da jami’an tsaro suka yi artabu da maharan tare da tura ƙarin jami’ai yankin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here