Home Siyasa APC: Bincikenmu ya nuna Tinubu zai lashe zaɓen 2027 – Yilwatda

APC: Bincikenmu ya nuna Tinubu zai lashe zaɓen 2027 – Yilwatda

5
0

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa binciken da jam’iyyar ta gudanar a jihohin Najeriya ya nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin wata tattauna wa a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels, inda ya ce ƙididdigar da APC ta tattara ta nuna Tinubu na kan gaba a gaban abokan hamayyarsa.

Ya kuma ce APC ba ta tsoron jam’iyyun adawa, ciki har da ADC mai alaƙa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da NDC mai alaƙa da Peter Obi.

Shugaban APC ɗin ya kwatanta Tinubu da Atiku, inda ya bayyana shugaban ƙasar a matsayin wanda ya fi tsohon mataimakin shugaban ƙasar ƙwarewa.

Yilwatda ya kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa sauye-sauyen haraji sun faɗaɗa yawan masu biyan haraji tare da ƙara kuɗaɗen shiga na gwamnati.

Ya kuma bayyana cewa gyare-gyaren da aka yi a ɓangaren wutar lantarki sun bai wa gwamnatocin jihohi damar samarwa, isarwa da rarraba wutar lantarki.

Dangane da tsadar rayuwa da tashin farashin man fetur, Yilwatda ya ce halin da ’yan Najeriya ke ciki na ɗan lokaci ne, yana mai cewa al’ummar ƙasar na ci gaba da amincewa da APC.

Ya ƙara da cewa jam’iyyar na duba jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, kuma za ta ƙaddamar da shi nan ba da jimawa ba.

Haka kuma, ya ce ba shi da matsala da duk wani mutum ko ƙungiya da ke son goyon bayan sake zaɓen Tinubu, yayin da ya yi watsi da gangamin “Tinubu Must Go”, yana mai cewa adawa ce ke ingiza shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here