Home Rahoto Sojoji sun kama ɗaya daga cikin shugabannin ‘yan bindiga a Zamfara 

Sojoji sun kama ɗaya daga cikin shugabannin ‘yan bindiga a Zamfara 

22
0

Sojojin Najeriya sun yi nasarar kama ɗaya daga cikin shugabannin ‘yan bindigar Zamfara wanda aka fi sani da Kacalla Halilu a wani samame da suka kai a Kasuwar sati-sati dake Shinkafi, bayan sun samu bayanan sirri.

Zagazola Makama mai bibiyar aiyukkan ta’adanci a yankin Chadi ya ce samamen da sojojin yanki na takwas suka kai ya faru ne bayan sun samu bayanan sirri na gaskiya wanda ake tuhumar yana cikin kasuwar.

Majiyar ta ce sojojin sun dira kasuwar a shirye suka cafke Halilu ba tare da yin wata ja-in-ja ba.

Kayan da aka samu a wurinsa sun haɗa da babur da wayar salula da hula da maganin dabbobi.

“Da aka baiwa sojoji labarin sirri ba su yi wata-wata suka yi aiki akai hakan ya sa suka yi nasarar kama wanda ake tuhumar,” a cewar majiyar.

A cewar Zagazola wanda ake tuhumar da abubuwan da aka samu a wurinsa an hannuta su ga jami’an kula da bayanan sirri na sojoji don cigaba da bincike.

Kamen da aka yi yana cikin yinƙurin da sojoji ke yi na ganin an kawar da duk wasu ‘yan ta’adda da ɓatagari a Zamfara da maƙwantanta dake yankin Arewa ta Yamma.

Jami’an tsaron sun ce bincike ne zai fito da yawan ta’addancin da yake da hannu ko masaniya da ake kan aiwatarwa.

Manema labarai sun ruwaito Zamfara na cikin manyan wuraren da harkokin ta’addanci suka ɗaiɗaita, jami’an tsaro suna aiki ba dare ba rana don ganin sun hanama ‘yan ta’adda rawar gaban hantsi a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here