Home Siyasa Gwamnatin Sakkwato ta rufe Ofishin Kamfe na ADC 

Gwamnatin Sakkwato ta rufe Ofishin Kamfe na ADC 

9
0

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta sanarda rufe ofishin yakin neman zaɓe na jam’iyyar ADC da ke Savannah Bank kan titin Ahmadu Bello a cikin birnin Sakkwato.

Kwamishinan Filaye da Gidaje Barista Nasir Aliyu Dantsoho ne ya sanarda hakan yau Litinin a lokacin da ya ziyarci ofishin tare da tawagarsa ya ce daga yanzu sun rufe ofishin har sai baba ta gani.

Ya ce sun rubutawa hukumar da alhakin kula da gidan don sanin matsayar mallakar gidan amma yanzu ba su samu bayani ba, kan haka gwamnati ta rufe wurin zuwa lokacin da bayani zai zo musu ko kuma mai mallakar wurin ya zo da takardun shedar mallaka domin tantacewa.

“Duk wani da ya saɓa wa gwamnati kan matakin ya shiga gidan ko yin wata mu’amala zai fuskanci Shari’a kan laifinsa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here