Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta TARA

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta TARA

20
0

RAUNIN RAYUWA

PP 9

‘Yar dariya ya yi a ransa ya ce ‘Ƙwaila jarabar duniya.’ Ya ci gaba da murmushi ya shige motarsa ya tada ita.
Ita kuwa Halisa bayan ta shige cikin babban soron gidan nasu ba ta wuce ba laɓe tana leƙen shi har sai da ta ga tashin motarsa tukunna ta mayar da kanta ciki tana jan siririn tsaki da taɓe baki.

“Wannan gayen kansa ba ya ja, maimakon ya lallaɓa ni ko kuma ya ba ni minti uku na fito shi ne har mintuna arba’in?” Ta yi wucewar ta zuwa sashin kakarta fuska ba yabo ba fallasa.

Ige ta idar da sallah kenan tana lazimi ta ji shigowar mutum faram-faram cikin ɗakin ana ta motsi kamar ana binciken kaya. Waiwayo wa ta yi ta ga ‘yar cakwanta ce take buɗe akwatinta da ke ajiye kan gadon ƙarfe mai rumfar da take kwanciya. Ƙure ta ta yi da ido ta ga tana faman zaro kayan sakawarta na ƙasan adaka, baki ta hangame kafin ta fara magana “Tofah! Yau ‘yar cakwaina ina ake shiri za a na ga ana ta hankaɗa tufafi?”

Ba ta daina abin da take yi ba kuma ba ta juyo ba ta ba da amsa “Hayat ne fa ya zo Ige yana ƙofar gida, shi ne nake so na caɓa ado na kece raini don ya tabbatar ni fa ba ƙaramar yarinya ba ce, ajina yana sama.”

Kama haɓa ta yi tana faɗar “Oh ni Ige jikar mutum huɗu wane ne kuma Hayatu?”
Wani lace ta ɗago cikin kayan sallarta na bara tana ƙare masa kallo lokaci ɗaya kuma ta sauyawa fuskarta shimfiɗa daga fara’a zuwa takaici mara zurfi.

“Habah Ige miye sai kin wani ɓata masa suna? Kin ma san shi kuwa? Kyakkyawan dogon saurayi da shi. Ki kira shi da Hayat in ba ki iya larabcin ba ki ce masa Rayuwa.”

“Toh! Rayuwa kuma? Wannan wane irin suna ne?” Kakar ta furta tana kama haɓa.

“Fassarar sunansa kenan tsohuwa, kin ga irinku tsofaffi da bakinku ba ya kama larabci sai ku faɗa da yarenku cikin sauƙi, amma dai kar a sake ɓata mini sunan saurayi.” Ta yi zancen tana ‘yar dariya haɗe da mayar da sauran kayan ta ajiye lace ɗin gefe ta dako tsalle ta sauko daga kan gadon.

Ige ta ɗora hannu a gefen wuya tana girgiza kai sauti a sama cikin ta’ajibi ta ce “Shehu Usmanu! Ke dai wannan yarinyar kina da matsala wallahi, yanzu saukowa daga gadon ne sai kin dako tsalle kamar namiji? Ba ki san ba a son mata da tsalle-tsalle ba?”

Ba ta kula kakar ba ta cire farin hijabin ta je waje ta ɗoro arwala ta shigo ciki da nufin yin sallah Igen ta sake tsare ta da zance. “Na ce shi wa ne ne wannan yaron da ya zo? Ɗan wace shiya ne a nan garin?”

Turo baki ta yi gaba ta wuce bazar-bazar ta ɗauko sallaya tana shimfiɗawa tare da faɗar “Ige shi ne fa wanda na ba ki labarinsa wata ɗaya da ya wuce na ce miki mun haɗu da shi a titin makarantarmu, ba har kwanaki ya kawo mini kyautar kayan kwalliya ba.”

“Af! Af! Haka fa, na tuna shi. To ina ce kin san ko ɗan wace shiya ne, kar fa ki janyo mana baƙon da zai cutar da mu.”

“Can fa yake cikin Mabera ta by pass, kin ga ai ko yayanmu za ku iya sakawa ya bincika muku asalinsa idan an tashi tun da shi ma a can yake?”

Da fara’a a fuskar tsohuwar ta ce “Haka fa ‘yar albarka, yi hanzari ki yi sallar ki ci gaba da shiri kar ki ajiye shi jira.”

Halisa ba ta sake tamkawa ba ta tada sallar, tana gama wa ta ci abinci a gurguje ta shiga wanka tana yi tana duba agogon ƙaramar wayar Ige, itel ce mai keypad.

Bayan ta gama duk wani shiri da za ta yi ta zura lace ɗin ta tsantsara kwalliyarta ‘yar daidai ta zauna tana jiran aiken shi.
Lokaci zuwa lokaci take danna wayar tana ƙara ganin lokaci, ta kasa zaune ta kasa tsaye, ji take kamar ta janyo lokacin da ƙarfin tsiya.
Duk abin nan da take a kan idanun Ige sai dai ba ta ce mata kanzil ba sai mamaki da take ta yi a ranta, ‘Wai yanzu yaran zamani haka suka lalace, su har sun san wata aba soyayya? Ita a zamaninsu ai ba ma ki isa ki san wanda za ki aura ba sai an kai ki, saɓanin na yanzu masu idanu a tsakar ka. Kalli yadda take rawar jiki har da caɓa ado wai za ta je zance.’

Sai da ya ƙara mintuna ashirin a kan yadda ya sanar mata sa’an nan ya aiko yaro a yi masa kiranta.
Ba ko wani ɗan jan aji ta miƙe bazar-bazar da rawar jiki ta ja mayafi za ta fita.

Ige ta kama haɓa. “Ikon Allah ikon gaskiya! To ai dai kya tsaya ki ji sharaɗina ko?”

Wata iriyar waigowa ta yi a shagwaɓe tana faɗar “Habah ‘yar tsohuwa miye matsalarki ne? Ni ki yi ki faɗi sharaɗin zan je in gan shi.”

“Sharaɗin shi ne ban da shiga motarsa, ku tsaya a soro sa’annan ki san yadda za ki yi idan ɗaya daga cikin ubanninki ya gan ki kina hira da rana tsaka ahto, ba ruwan Ige jikar Hausi.” Ta janyo goron da ke kusa da ita ta ɗauki magogi ta naɗe ƙafafuwa zaman tama-tela ta fara goga shi a jikin magogin ƙarfe ƙarami irin na da wanda aka ƙera da marfin gwangwanin madara.

Ba ta ce komai ba ta kama hanya za ta fice daga ɗakin kenan yaron baba Bello mai suna Sagir ɗan shekaru sha biyu ya shigo da kulolin abinci. Kafin ma ya kai ga ajiyewa har ya gayar da kakarsa Halisa ta yi wuf ta buɗe kular da ke rungume a ƙirjinsa. Cinyar kaza ta gani a kan lafiyayyiyar soyayyiyar shinkafa, ba jira ta kai hannu ta ɗauke cinyar ta hau ta da cizga. Can kuma kamar wacce aka yi wa wahayi ta mayar da kazar kan shinkafar ta yi waje tana lashe hannu da faɗar “Ki fa ajiye mini kasona ‘yar tsohuwa ina dawowa.” Ta yi gaba abin ta ba ko waiwaye.

Ige ta girgiza kai tana faɗar “Kuma haka za ki fita hannu duk maiƙo? Wannan yarinyar ban san sai yaushe za ki san kin fara girma ba.”

Zancen da take yi sai ya zama tamkar ihu bayan hari don wacce take zancen da ita tuni ta yi gaba da alama ta ma manta da maiƙo a hannunta da bakinta.

Tana leƙowa ta gan shi daf da ƙofa a waje sai ta yi masa alama da ya shigo zauren, bai ƙi ba ya saka kai ciki. Tsaye ya yi yana ƙure ta da kallo daga fuska zuwa ƙasa kamar zai yi dariya sai kuma ya ƙume kayarsa.

ƁANGAREN FATIMA

A wannan satin Fatima ta rayuwa da mijinta cikin soyayya da mutunta juna har ta ji ranakun suna yi mata kama da ranakun amarcinta, ba ta da wata matsala ko ɗaya daga ɓangaren cimaka, sutura da kayan more rayuwa, daidai gwargwado duk abin da take buƙata ya tanade shi, idan ma babu yakan nemo mata cikin ƙanƙanin lokaci.

Rayuwa mai daɗi suke shimfiɗawa cike da ƙaunar juna har ta soma manta wa da uƙubar da ya shayar da ita a kwanakin baya. Bayan sati ɗaya ta samu tsarki daga jinin biƙi a wannan ranar ne kuma ta koma asibiti don a sake duba ta ko ba wata matsala.

Washegarin ranar da misalin ƙarfe takwas da arba’in da biyar na safiya zaune suke a kan center carpet suna yin breakfast, can Fatima ta yi kamar ta tuna da wani abu ta kalle shi “Yauwa yaya don Allah idan ba damuwa an jima da yamma ina neman izini zan je gidan biki akwai ƙawata Mardiyya da take a Barhim estate yau ake ɗaurin aurenta tun wata ɗaya baya take jaddada mini zancen bikinta a wannan satin.”

Sai da ya gutsiri biredin hannunsa ya kora da tea ya haɗiye kafin ya ce “Shi kenan ba damuwa na yi miki izini.”

Da murmushi a fuskarta ta ce “Na gode yaya, ina neman ƙarin alfarma tun da yau Sunday ba aiki don Allah ka taimaka ka kai ni idan ya so na dawo a ɗansahu.”

Kallon cikin ido ya yi mata ya ƙara kurɓar shayinsa a karo na biyu sai da ya gama wani ɗan nazari kafin ya ce da ita “Ki yi haƙuri sweetheart ba zan samu damar kai ki ba, yau da wannan lokacin muna da tattaunawa da abokanmu su Hafiz da Ahmad da sauran tawagarmu, kin san na faɗa miki wata mai kamawa za a yi auren Ammar Ahmad abokinmun nan da muka yi jami’a tare, to shi ne za mu yi zaman tattaunawa kan tsare-tsaren bikin.”

Jikinta ya yi sanyi da jin wannan zancen sai dai ba ta fusata ba tun da ya bayar da uzuri bikin magaji ai ba ya hana na magajiya ba sai kawai ta ce da shi “To shi kenan ba komai ai sai in tafi a ɗansahun.”

Ta ajiye kofin hannunta tana miƙewa za ta bar gun, ya yi wuf ya kama rigarta ta baya ta waigo da mamaki a fuskarta.

Bai jira ta yi magana ba ya riga ta da faɗar “Fatan dai ban ɓata miki rai ba.”
Fuskar ta ta bayyanar da murmushi ta girgiza kanta murya a ƙasa “Uhm! Ko ɗaya.”
Ya sake mata rigar yana faɗar “To idan ba komai me ya sa kika tashi za ki bar gun muna magana?”
“Kawai dai na kammala ne ina so in shiga ciki akwai abin da zan yi.”

Tana gama faɗa tasa kai ta yi gaba, jikinsa ya yi sanyi gani yake kamar ba ta ji daɗin hakan ba. Da a ce yana da damar take wancan uzurin ya yi nata da ba abin da zai hana ya yi mata hakan, sai dai kash ba ya tunanin zai yi wannan saken da zai ɓarar da damarsa.

A gidan biki taro ya haɗu gida ya cika fam ta ko ina ka juya mata ne tsakanin dangi, ƙawaye da abokan arziƙi sai shige da fice ake, ko wacce ka gani ta caɓa adonta daidai da ra’ayinta.
Amarya Mardiyya ta ci ado cikin atamfa ‘yar golden kalar skyblue mai ɗaukar hankali ta yafa farin mayafi tana sanye da fararen takalmi da jaka ta fito daga cikin gidansu riƙe da hannun Fatima yayin da wasu ƙawayenta biyu ke take musu baya suka jero suna hirarsu irin ta ƙawaye gwanin burgewa. Sun fito ƙofar gida kenan suka ci karo da Farida ta taho da gudu ta rungume Fatima tana faɗar “Wayyo Allahna! Fatima ashe rai kan ga rai.”

Buga kafaɗarta Fatima ta yi tana murmushi “Wallahi kuwa, ga shi dai mun haɗu, aka ce wai hanya mai haɗa zumuntar dole. Yanzu da ke kin shigo garin nan kin san a nan nake aure shi ne kuma ko ki neme ni?.”

Farida ta raba jikinta da na Fatima tana faɗar “Ke ma dai kin san idan ina da hanyar neman zan neme ki, bayan aurenki da shekara uku ne aka turo ni nan garin karatu, ina zaune ne a gidan ƙanwar mamana. To tafiyar ce ta taso mun ta gaggawa na ma sha’afa da cewa a nan aka kawo ki. Da na tuna ai da na je gidanku na samo lambarki duk da na taɓa zuwa aka ce innarku ta yi aure a Kudu ta koma can da zama.”

Sai a lokacin Farida ta haɗa ido da Mardiyya ita kuma ta aika mata harar wasa tana kauda kai gefe.
‘Yar dariya Faridan ta yi ta matsa kusa da amaryar cikin taushin murya “Yi haƙuri amarya, ya hidimar?”
Ta sake hararar ta kafin ta yi murmushi mai sauti “Hidima alhamdullillah, ai na ga kun manta da ni ne wata ta ga wata. Wai ma a’ina kuka san juna?”

Ta yi zancen tana riƙe hannun Faridan da hannu hagu yayin da hannun damanta ke riƙe da hannun Fatima ta fara jan su suna takawa zuwa gidan da take zaman amarci da ƙawayenta. Yanmatan da ke take mata baya su ma suka ci gaba da bin su.

Farida ce ta ba wa amarya amsarta da faɗar “Tare fa muka yi ƙaramar secondry a Sokoto, kujerarmu ɗaya da ita a lokacin tamkar ‘yan biyu muka kasance har yan aji suna yi mana take da idan ka ga raƙumi ka ga Buzu. Sai dai muna kammala jlce ni na canza makaranta zuwa wata ita kuma ta ƙarasa a nan to tun lokacin ya zamana idan ina son ganin ta sai dai na je mata gida ko ita ta zo mun a duk san da ta yi ra’ayi.”

“Kai! Ah! Lallai ashe daɗaɗɗiyar alaƙa ce, da alama kun kai shekara huɗu ba ku haɗu ba ma.” Daidai nan suka shige gidan. Farida ta amsa da “Shekaru shida kenan.”

Sun tarar da ‘yanmatan amarya da yawa a cikin gidan sun yi tawaga-tawaga wasu a waje wasu a ɗaki kan kushin wasu a gefen gado suna cin abinci ana ta raha da farinciki. Wuri suka samu a uwar ɗakan kan gado suka zauna suna ci gaba da hirar yaushe gamo.

Can wuraren ƙarfe biyar da arba’in na yamma Fatima ta ari wayar amarya ta kirawo Musa a waya take shaida masa ta gama da gidan bikin ko zai zo ya maida ta gida? Sai ya nuna mata cewa ta dai ƙara haƙuri yana riƙe ne a kan wani uzuri. Kashe wayar ta yi ta goge lambar ta miƙawa Mardiyya ta kalli ƙawayen nata biyu, “To ni fa ina ganin zan lallaɓa yamma ta yi.”
“Ah! Ba mijinki zai zo ya ɗauke ki ba?” Cewar Farida. Fatima ta girgiza kai alamar a’a “Uzuri ne ya riƙe shi ba zai samu zuwa ba.”

“Ayyah! Na so a ce zai zo mu gaisa ko don ma na ga wanda ya ɗauke mini ke zuwa wata uwa duniya.”

Ta yi ‘yar dariya tana miƙewa tare da gyara zaman mayafinta da jakarta.
“Kina ji, gaskiya ba zan bari ki tafi a ɗansahu ba. Bari masoyina ya zo sai mu tafi tare ya fara sauke ki, da ma a ɗazun ma shi ya sauke ni gidansu amarya Munnira na fara ta can sannan na ƙaraso nan.” Ta yi zancen tana ƙoƙarin buɗe jakarta, ta ciro wayarta da ke ciki ta fara daddannawa.

Fatima ta yi murmushi ta koma ta zauna inda ta tashi da fari tana faɗar “Inyeah! Ka ji manyan ‘yanmata masu zamani, ina ce wannan ɗin dai da shi za a yi ko?”

Ita ma murmushi ta yi ta ce “Uhmm! To har yanzu dai ban gama tantancewa ba, idan dai yana da rabo sai ki ga an yi da shi ɗin, don ba laifi daidai gwargwado ya mallaki fiye da rabin qualities da nake nema a gun namiji kuma yana sakin masu gidan ranar, yana hidimta mini sosai yake nunan ƙauna.”

Fatima ta yi dariya tana faɗar “To Allah ya sanya alheri, bari na jira na ga waye wannan ɗan sa’ar.” Rufe bakinta ya yi daidai da lokacin da aka ɗaga layin da Faridar ta kirawo don haka ta kanga a kunnenta ta karye harshe cike da salo tana faɗar “Assalamu alaikum masoyi ka ga na sake kiranka ko?”

Shiru ta yi na ɗan gajeren lokaci sannan ta sake cewa “Eh wallahi, da ba yanzu zan wuce ba sai after magrib shi ya sa na faɗa maka hakan, amma yanzu na sauya ra’ayi ka zo yanzu kawai ka mayar da ni gida.”

Ta sake yin shiru na sakanni kafin ta sake cewa “To masoyi sai ka zo. Bye I love you.”

Ta gimtse wayar ta kalli Fatima fuskarta cike da fara’a ta ce “Ya ce ma yana ta kusa-kusa da nan daga yanzu zuwa kowanne lokaci za ki iya ganin shi.”

“Allah ya kawo shi lafiya.” Shi ne kaɗai abin da Fatiman ta faɗa suka ci gaba da hirar duniya. Can bayan mintuna sha biyar ya kira ta ta kwatanta masa daidai gidan sai ga shi kuwa ya hallara.

A tare suka fito gidan da Fatima ita tana gaba Fatiman na biye har zuwa gaban motar, sai dai tun da suka fito ƙofar gida Farida ta nuna mata motar da hannu gabanta ya faɗi. Ko a mafarki ta ga wannan motar ai za ta shaida ta, amma an ce wai idan ba ka iya kama ɓarawo ba shi sai ya kama ka.
Don haka cike da ƙarfin gwuiwa da yarda da shawarar da zuciyarta ta kitsa mata ta ci gaba da bin ta har gun motar.
Faridan ce ta leƙa ta gilashin da ya sauke na ɓangaren mai zaman banza suka gaisa sama-sama ta ce da shi “Yauwa masoyi don Allah idan ba damuwa za mu sauke ƙawata a gidanta, mijinta ne ba zai samu zuwa ɗaukar ta ba.”

Saƙon murmushi ya aika mata kafin ya ce “Ah! Ba damuwa idan dai hanyarmu za ta yi ɗaya.”
“Kai amma dai na gode masoyi.”
“Uhmm! Kar ki damu komai zan iya yi saboda ke.” Murmushin narkar da zuciya ta watsa masa kafin ta juya ta kalli Fatima ta yi mata nuni da gidan baya. “Bismillah ƙawata.”

Ba musu Fatima ta buɗe motar ta shige zuciyarta na yi mata zafi sosai. Da gayya ta ware murya tarwai ta ce da shi “Sannu angon ƙawata, ina wuni ya aiki?”

Tun kafin ya waigo ya ji zuciyarsa na tsalle kamar za ta fasa ƙirjinsa ta fito, ya yi hanzarin waigowa don tantance saƙon da zuciyarsa ke yi masa barazana da shi ta hanyar kunnuwansa da suka zuƙo sautin muryar matarsa.
Idanunsa ya sauka cikin nata ya lura da yadda ta ƙanƙance ido fuskarta ta sauya, tashin hankali ya bayyana ƙarara a fuskarsa ya juya gaba ya kalli gefensa kenan ya ga Farida ta shigo ta rufe ƙofar tana faɗar “Masoyi ga ƙawata ku gaisa, alaƙarmu tun ta shekaru goma baya ce.”

Diri-diri ya yi kafin ya gayyato nutsuwa zuwa jikinsa ya yi ƙarfin halin shimfiɗa fara’a a fuskarsa bai juya ba ya yi magana da murya mai rauni “Sannu ƙawarmu, ya iyali?”

Daurewa ta yi ita ma ta yi kamar ba ta taɓa sanin shi ba ta amsa da “Lafiya qlau alhamdullillah.” Sannan ta ƙara da faɗar “Ga amanar ƙawata nan don Allah ka kula mini da ita sosai.”
Bakinta ne ya furta amma zuciyarta ke azabtuwa da zafin furucin.

Ba yadda ya iya haka ya tada motar suka fara tafiya Farida na ta jan shi da hira sai dai sam ba nutsuwa a jikinsa sai pretending kawai yake yi daga um sai um-um.

Can ta juyo ta ce da Fatima yauwa wace unguwa za a sauke ki. ‘Ya fi ni sanin unguwar ai.’ Wannan ne abin da zuciyarta ta raya mata ta faɗa amma wannan karon sai ta yi rashin biyayya ga zuciyar ta kwatantawa Farida arear. Har ƙofar gida suka sauke ta, Farida ta juyo ta ce da ita. “To ƙawata sai yaushe kuma?”

“Uhmm! Ƙila sai zumuntar gidan biki ta sake haɗa mu don ban ga alamar kina da kirkin da za ki kawo mini ziyara ba.”

Dariya ta yi sosai daga gaban motar take cewa “Ba fa haka ba ne, yanzu ma don a hanya nake ina sauri ai da na shigo na ga ɗakinki. But kar ki da mu na ga gidan ai, zan dawo watarana.”

Dariyar yaƙe ta yi ta buɗe murfin motar ta fita tana ɗaga wa Faridar hannu da faɗar “Allah ya kawo ki lafiya.” Sannan ta leƙo ta saman gilashin ɓangaren da Faridar ke zaune ta ce da shi “Na gode sosai da karramawa da mutuntawa angonmu, Allah ya sauke ka lafiya. A gaida iyalin idan akwai.”

Ba ta jira amsar da zai bayar ba ta shige gidanta cikin ƙuncin zuciya.

Ummu Intisar ce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here