Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 28

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 28

13
0

Na

Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Intisar)

Ahalin paid group ina miƙo gaisuwa, marasa lafiya Allah ya ƙara muku lafiya, ma su karatu Allah ya bada nasara.

AREWA WRITERS ASSOCIATION

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

ƁANGAREN FATIMA

PP 28

Cikin yanayi na rashin makama ya miƙe ya shiga wanka bayan ya fito ya zo falo ya zauna ya buɗe kulolin don cin abincin har zai fara ya yi jim kamar mai tunani sai kuma ya rufe ya miƙe tsaye. Ita kuwa tana ganin hakan kamar wacce ta shiga tunaninsa ta san dalilin rufe abincin ta yi hanzarin cewa “Sajidah ce ta yi girkin na dai taya ta ne kawai.”

Ya ɗago kansa ya watso mata wani irin kallo mai nuni da cewa akwai magana a bakinsa, laɓɓansa na motsi alamar zai yi magana ko me ya tuna sai kuma ya yi ɗif ya sake buɗe ya fara cin shinkafar.

Zaunawa ta yi daga can gefe tana kallon ɓangaren hagu, ita da shi ba wanda ya sake magana kowa da bikin zuciyarsa. Shi yana tunanin me Sajidah za ta iya sani bayan zuwan ta gidan, bai yi magana ba ne don ya san muddin akwai wani abu a ƙasa zai ji idan ya je gida yau. Ita kuma tana tunanin ya za ta ɓullo masa da lamarin abincin da take buƙata.

Ita ce ta fara juyawa ta kalle shi cikin dauriya ta ce “Yaya ina jin yunwa don Allah ka taimaka mini ko da taliya ne, kuma ina son na sha mangwaro nunanne don Allah.”
Motsin bakinta ya bi da kallo lokaci da take furta nunanne, lallai sai yanzu ya tabbatar yarinyar nan ba ta da kai ya kamata ya yi maganin iskancinta in ba haka ba sai ta raina shi.

Cokalin ya sake da ƙarfi ya daki farantin ƙashin ya ba da wata ƙara gyaram ya miƙe a fusace zai bar gun kenan ta sake furta “Don Allah yaya ka taimake ni tun safe ba komai a cikina. Azababbiyar yunwa nake ji.”

Ya juyo da idanunsa da suka fara ƙanƙancewa don ɓacin rai ya daka mata tsawar da sai da ta razanar da ita “Ke! Buɗe kunnenki ki ji ni da kyau. Ba ni na ce ki ɗauki ciki ba a gidan nan ballantana na yi tolerating tsirfinki. Idan kin ga dama ki ci abin da nake ci idan kuma ba za ki iya ci ba ki nemi wata mafitar ni dai na fita haƙƙin ciyarwarki.”

Yana gama faɗa ya fara takawa zai shige ciki suka jiyo sallama daga ƙofar ɗaki hakan ya saka shi tsayawa cak tare da juyowa kafin ma a amsa sallamar tuni yarinyar da ba za ta fi shekara bakwai ba ta faɗo ɗakin tana fuskantar Fatima da faɗar “Anti Amarya wai in ji innarmu yaya ya ce an turo miki kuɗin ki zo a cire miki.”

Kallon tuhuma ya fara watsa mata ta lura da hakan dalilin da ya sa ta ɗauke kanta ta yi kamar ba ta gan shi ba ta dafa kafaɗar yarinyar tana faɗar “Kina ji Suhaila daga yau in kin zo ki tsaya daga ƙofa ki yi sallama sai idan kin ji an amsa an ce ki shigo sannan ki shigo ciki kin gane?”

Yarinyar ta gyaɗa kai alamar eh, sannan ta sakar mata murmushi tare da janye hannunta a jikinta tana faɗar “Ki cewa Inna zan shigo na amsa.”

Tana rufe baki yarinya ta juya ta fice daga gidan. Fatima ba ta bi ta kansa ba ta yi hanyar uwar ɗakanta, muryarsa ta tsinto yana faɗar “Wa ya turo miki kuɗi?”

Ba ta ba shi amsa ba kuma ba ta da niyyar juyowa sai gani ma ya yi tana ci gaba da nufar inda ta yi niyyah, hakan ya sa ya yi hanzarin matsawa inda take ya cafko mata hannu ta baya ya matse da ƙarfi cike da mugunta ya kafa mata farata a jikin fatar wuyan hannun.

“Shii!” Ta saki sauti mara ƙarfi ba dai ta juya ɗin ba ta kafe a gun tana jiran ganin me zai faru.
“Da ke nake magana, wa ya turo miki kuɗi?”

“Innata!” Ta ba shi amsa a gajarce.

Sake mata hannu ya yi ya tsaya sororo yana mai furta “Ƙara ta kika fara kai kenan? Da me na rage ki da shi da za ki fara maula? Ta fi ma kin yi maular mahaifiyarki ce, me ya sa ba za a tura miki a account ɗina ba sai na wani ƙaton a waje?”

Ko ɗaya daga cikin amsoshin ba ta ba shi ba ta shige ɗakin ta banko ƙofar daga ciki.

A ƙofa ya tsaya yana huci da furta “Kar ki sake ki fita gidan nan da sunan zuwa don karɓar kuɗin nan, idan kuma kika je ba da yawuna ba.”

Daga ciki ta jagaɓe a jikin ƙofar tana jiyo muryarsa yana fama da masifa a ƙofa sai hawaye ke zuba a kuncinta wani na korar wani.

Da gaske har cikin ranta ta fara jin gajiyawa da wannan auren, ta fara nadamar baro mahaifarta, ba ta jin idan za ta jure komai za ta iya jure horon yunwa ga shi kuma ya fara ƙoƙarin toshe duk wata kafa da za ta sama mata sauƙi. Ya yake so ta yi da rayuwarta? Ita ba dangin iya ba na baba a gari, ba ta da kowa sai Allah da mutanen arziƙi wa za ta je ta kai wa kukanta don ya share mata?

Ba shi ya fice gidan ba sai gaf da la’asar ya yi arwalla ya wuce masallaci daga can kuma ya buga cikin gari, leƙa nan leƙa can har shida na yamma ya wuce gidansu.

Zahiri yana jin fargaba a lokacin da ya kusanci gidan har kamar ya juya ya koma amma sai ya dake ya ƙarasa yana so ya san ko me ake ciki don ya san matakin da zai ɗauka a kai.

Da sallamarsa ya afka falon inda ya sami Hajiya mama zaune a kan doguwar kujera ta miƙe ƙafa da carbi a hannunta tana lazimi ya je kujerar kusa da ita ya zauna yana gaishe ta. “Sannu da gida Hajiya mama.”

Da fara’arta ta amsa masa da “Yauwa sannu mai sunan malam, ya gidan da kuma mai jiki?”

Ras ƙirjinsa ya buga sai ya yi kamar bai fahimci komai ba ya ce da ita “Wani ne ba lafiya?”

Murmushi irin nasu na dattijai ta fesa masa kafin ta ce “Mai sunan malam kenan, wato dai kana jin kunyar ka sanar da ni. To magana nake a kan ‘yata Fatima. Ɗazu na tura Sajiidah gidan ta duba mini lafiyarta shi ne ta dawo mini da labari mai daɗi. Da ma nan zaman jiranka nake ka zo ka kai in duba ta.”

Ta yi zancen tana yunƙurin miƙewa shi kuwa bai ce komai ba sai ƙasa da ya yi da kansa yana jin ɓacin rai na kawo masa ziyara. Ko me Sajidan ta gano da ta zo ta ba da labari har yau Hajiya mama da kanta take shirin zuwan gidan? Ba ɗabi’arta ba ce zuwa gidan sarakanai sai dai su je gidanta su same ta. Duk uzurin da ya saka ta taka gidan sirika ko siriki ba ƙaramin abu ba ne.

Bai san dalilin jin ɓacin ran ba yana ji dai cewa hakan ba ya rasa alaƙa da jin haushin Sajidan da ya yi, ya tabbatar ita ta ce ta naɗo rahoton gidansa ta zo nan ta baje.

Da a ce ta kama bakinta da abin da ta gani da ba za a zo wannan matakin ba. Yana nan shiru yana ta saƙe-saƙen dabarar da zai yi ya hana Hajiya mama zuwa gidan nasa sai ga ta ta fito sanye da gogaggen hijabinta da tabaraun ƙara gani (medical glass) tana faɗar “Ta shi mu je, so nake ka mayar da ni kafin magariba.”

Ya miƙe kamar wanda aka zarewa lakka yana shafa sajen da ke kwance luf a haɓarsa. “Am! Hajiya da ma kin bar shi, ai jikin nata bai yi wani tsanani ba.”

“Na ji shige dai mu je.” Ta yi maganar cikin ba da umurni fuskarta ba alamun wasa a tattare da ita wanda hakan ya tabbatar masa da cewa ba shi da wata matsera don haka kawai ya gyaɗa kai yana faɗar “To hajiya, mu je motar tana ƙofar gida.”

“Ai na sani, yi gaba ga ni nan bayanka.”

A cikin baranda suka yi kiciɓis da Sajidah ya watsa mata wata muguwar hararar da ya saka ba shiri ta sadda kanta ƙasa hannu na kakkarwa. Zai yi magana kenan suka jiyo muryar Hajiya mama a bayansu tana faɗar “Ke Sajidah zo nan.”
Sauri ya yi ya wuce ta ba tare da ya fitar da ta cikinsa ba don gudun abin da ka iya faruwa idan maman ta ji. Ita ma kamar jiran kiran take ta amsa da “Ga ni nan zuwa.” Ta shige ciki da hanzari.

A kofar ciki suka haɗu har ta tashi ture Hajiyan saboda yanayin shigowar da ta yi a tsorace. Hajiya mama ta kalle “Ke lafiyanki kuwa?”

Ta yi gaggawar girgiza kai alamar a’a sai kuma ta girgiza alamar eh duk a lokaci ɗaya.

Ta lura da yanayinta amma da ke tana sauri ba ta son a ɓata mata lokaci ya sa kawai ta ce da ita “Zan je gidan yayanku yanzu, ki kula da gidan. Idan Hashim ya zo ya jira ni ba jimawa zan ba.”

Ta yi alamar ta fahimta da kai kafin ta ce “To Allah ya tsare hajiyata.”

Ta amsa da amin ta fita ta tarar da shi zaune cikin mota yana jiran ta, sai da ta tsaya ta gaisa da mazajen da ke makwaftaka da ita da suka taso suna gaida ita kafin ta shige gidan baya ya ja motar.

Bai yi birki a ko’ina ba sai a ƙofar gidansa ya kashe motar. Yana ta sauri ya riga Hajiya mama shiga gidan don ya gargaɗi Fatima, amma haƙarsa ba ta cimma ruwa ba don kuwa ta riga shi yi gaba dole ya bi bayanta ƙirjinsa na tsananta bugawa.

Da sallama ta shiga gidan lokacin Fatima ta kammala sharar yamma tana zaune a tsakar gidan ta tasa ragowar taliyar da ta saka Zinat ta sayo mata a gaba tana ci.

Zinat ɗin ce ma ta tsaya ta dafa mata taliyar don ganin halin galabaitar da take ciki. A ɗazun ta ci rabi ta ji ya fara haye mata zuciya sai ta aje, shi ne yanzu ta ɗauko ragowar ta zauna tana ci sai ga shigowar hajiya mama da sallama.

Cikin sauri ta rufe abincin ta miƙe ta wanke hannunta ta nufo Hajiyan da murna tana faɗar “Sannu da zuwa hajiyanmu.”

Fuska cike da annuri ta amsa da “Yauwa sannu ‘yata ya gidan?”

“Lafiya lau alhamdullillah! Bismillah Hajiya.” Har a lokacin kanta a ƙasa yake ba ta yarda sun haɗa ido da ita ba ta yi gaba tana ɗage labule, Hajiyan ta shige ta bi ta ciki ta zauna a ƙasan tiles suna ƙara gaisawa.

Lokacin ya shigo ciki yana faɗar “Bari na tashi inji Hajiya.”

“A’a bar shi in dai don ni za ka kunna, zo nan ka zauna. Ina da magana da ku.” Abin da yake ƙoƙarin gujewa kenan sai ga shi kamar ta harbo jirginsa ta hana shi zillewa.

Zaunawa ya yi daga gefenta na hagu yayin da Fatima ke zaune a gefen dama. Sunkuyawa hajiyan ta yi ta kamo hannayen Fatima guda biyu tana ƙoƙarin ɗago ta sama da faɗar “Yata taso, zauna nan kusa da ni.”

Ta yi zancen tana nuna mata gefe da ido ba ta saki hannunta ba har sai da ta tabbatar ta zaunar da ita inda take muradi. “Ya jikin naki?”

Ta yi ƙasa da kai tana jin bargon kunya na rufe ta. Murya ƙasa-ƙasa ta amsa da “Na ji sauƙi.”

Da dabara hajiyan ta duba hannunta ta kalli cikin ƙwayar idanunta da kyau har ta ƙara tabbatar da abin da ta fara jin lallai akwai shi tun farkon sauke magananta a kan sirikar tata, ta ga yadda ta rame ta yi fayau da ita. To a yanzu da ta ƙara duba
ragowar alamomin ta samu cikakken tabbaci a kai nan da nan farinciki ya mamaye fuskarta har bakinta ya kasa rufuwa sai da ta ce “Masha Allah! Allah ya raba lafiya ya sanya wannan rabo ne.”

A can ƙasan ran Musa ya ce ‘Shi ɗin ma ba rabo ba ne, kwanan nan zai bar jikinta ya bi sauran ‘yan’uwansa ba zan iya ba.’

Ba wanda ya amsa mata addu’ar a cikinsu hasalima kasa ɗago kai Fatiman ta yi sai Hajiyan ce ta sake cewa “Mai sunan malam!”

Ya ɗago kai murya a ƙasa tamkar munafiki ya amsa “Na’am hajiyata.”

“Umurni ne ba shawara ba ka shirya mu je asibiti ni da kai da ita mu gabatar da ƙorafi a gun likita kan yawan faɗuwar cikin da take samu. Idan ta kama ma su ɗaure cikin a zaunar da ita guri ɗaya har sai ta haihu. Koma dai me za su yi ina son a haife wannan.” Ta yi zancen tana nuna cikin Fatima ba alamun wasa a cikin kalamanta.

“Tabɗijam! Da ma ba shi yake ɓarar da sauran cikin ba…”

Ba ta fuskanci cewa a fili ta yi zancen ba sai da ta jiyo sautin Hajiyan cikin tashin hankali tana furta “Me kika ce? Shi yake ɓararwa?”

Ba ja kare ya mutu a saura ta riga ta tabbatar da ta yi katoɓarar da za ta iya kawo ƙarshen igiyar aurenta, ba ta san lokacin da hawaye ya zo mata ba ta dai ji saukar shi a kan kuncinta. Ta sani cewa idan za ta cika duniyar nan da rantsuwa Musa ba zai taɓa yarda cewar ba da gangan ta tona asirinsa ba.

Furucinta na ratsa tsakiyar dodon kunnensa ji ya yi kamar an kwafɗa masa guduma a tsakar ka. ‘shi kenan ta kashe ni da raina.’ ya yi zancen a zuciyarsa bai iya ɗago idanunsa ba don yana tsoron abin da hakan zai janyo masa.

Da Hajiyar ta ji duk sun yi tsit kamar ba rayayyi a gun ta sauke idanunta a kansa cikin tsananin fushi “Musa ɗago idonka ka kalle ni.”

Cikin wani irin hanzari ya tada kai ya saka idanun nasa a natan, ba wai don umurnin da ta ba shi ba sai don firgicin sunan da ta kira shi da shi wanda tun tashin shi bai taɓa jin ta faɗi sunan ba ko ga wani ballantana a ce shi ta kira da sunan, don kuwa sunan sirikinta ne wato mahaifin mahaifinsa. ‘Lallai rana ta ɓaci. Shi ko me zai yi wa Fatima ya fanshe wannan al’amari?’

Da murya mai kaushi ta fara magana “Da gaske kai kake ɓarar da duka cikin da ta taɓa samu a baya?”
Cike da ruɗewa ya girgiza kai da nufin ya yi alamar a’a ya fara yin ta eh kafin ya gano ya kwafsa ya sake girgiza wa yana ƙaryata kansa da faɗar “A’a , a kan..kan me zan.. zan aikata hakan ga jinina?”

Yanayin yadda yake bayar da amsa cikin in-ina da rikicewa ya sa Hajiyan ta ji a ranta matar ta fi shi gaskiya, ji ta yi farashin ɓacin ranta na ninkuwa.

“Wannan wane irin rashin hankali ne? Kai ba a haihuwar na haife ka? To bari ka ji in faɗa maka wannan karon zan zuba ido a kai, wallahil-azim duk abin da ya sami ɗan cikin nan sai na yi shari’a da kai idan ni ba ka tsoron hukuncina ai na san dole ka ji tsoron na alƙali.”

Ta yi shiru ran ta ya yi ƙololuwar ɓaci, ya san wace ce hajiyarsa idan ranta ya ɓaci bakin rijiya ba wajen wasar makaho ba ne.
Wannan ba lokacin ƙoƙarin kare kai bai ne lokacin neman mafita ne domin ta riga ta faru ta ƙare an yi wa mai zani ɗaya sata.

Ƙara ƙanƙan da kai ya yi ya fara magiya “Don Allah Hajiya ki yi haƙuri kada ki yanke hukunci cikin fushi, daga ba ya za ki fahimta…”

“Au! Har yanzu ƙoƙarin kare kanka kake?” Ta furta da zafi kaɗan a muryarta.

Ya girgiza kai alamar a’a a ruɗe ita kuma ta miƙe tsaye tana kallon Fatima “Yata ni zan koma Allah ya ƙara miki lafiya da haƙuri.
Idan bayan tafiyata ya yi miki wani abin ki zo gida ki same ni ki sanar da ni zan sama miki adalci, ke amana ce a wurina. Kada ki ji tsoron zuwa ni na ba ki izini.”

Ta mayar da dubanta inda yake tsaye jiki na kakkarwa kamar wanda aka watsawa ruwa a lokacin hunturu. “Shige mu je mutumin kawai…”

Ai tun kafin ta rufe baki ya juya ya bi hanyar waje ta take sawayensa tana ci gaba da faɗar “Ai wallahi ka ban mamaki ban taɓa zaton za ka aikata jahilci irin wannan ba.”

Har suka je bakin mota tana bisa ga bakinta tana ta masifa abin ka da mai haƙuri idan aka ƙure shi. Shi dai ba abin da yake sai aikin ba ta haƙuri har suka shiga motar ya tada.

Ita kuwa Fatima suna fita ta ɗora hannu a kai ta rasa abin da za ta yi, ta ma kasa yin ihun ji take kamar yau alkiyamar rayuwarta ta tsaya ba tare da zuwan mutuwarta ba. Tsoro take ji sosai na abin da zai biyo baya har wata zuciyar ta shawarce ta da ta tashi ta rufe ƙofar gidan kafin ya dawo don ta san yau sai ta fi sakwarar hannun Bayarabiya kirɓuwa.

A bayyane ta furta “Yau tawa ta same ni kura da hatsin gandu.”

To fah! Shin Musa zai zubar da makamansa?

Me zai faru ga auren Fatima?

Shin a ganinku ta yi daidai ko kuma kuskure ne tona asirinsa?

Ummu Intisar ce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here