Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 16

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 16

14
0

NA

Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Intisar)

Godiya; Godiya da jinjina ta musamman a gare ku Malama Shafa’atu da Maman Zarah, ina jinjina muku kan namijin ƙoƙarin bibiyar wannan labari da yin sharhi a kullum ba gajiyawa. Fatan Allah ya sa mu amfana da abin da ke cikin wannan rubutun.

PP 16

A cikin sati ɗaya sai da Ahmad ya yi ƙoƙarin mantar da Surayyah rabin damuwarta da ƙwarewarsa a fannin soyayya, sai da ya sa ta ji tamkar ba ta taɓa kasancewa a cikin soyayya ba tsawon rayuwarta sai a yanzu. Duk wata kulawa da ya cancanci masoyi ya ba wa masoyiyarsa Ahmad yana yin iyakacin abin da zai iya yi da aljihunsa da ƙarfinsa don tabbatar da farincikinta, har waya sai da ya saya mata babbar Android ƙirar infinix zero x wadda ta fita a farkon shekarar. Wani abun burgewa a tare da shi shi ne, bai karɓi ta hannunta ba kuma bai faɗa mata farashin wayar ba, ta nuna kawaici yayin amsa sai dai da ya dage ta karɓa da amincewar iyayenta sai bayan aikata hakan ta bincika kuɗin wayar, ta ji cewa a lokacin kuɗin sun kai kimanin Naira dubu ɗari da hamsin.

Ta ji matuƙar mamaki da irin wannan kyauta a sati ɗaya kacal da haɗuwa don haka daga shagon da aka faɗa mata farashin ta wuce gidansu Maryam cike da farinciki ta nuna mata wayar tare da ba ta labarin komai. Maryam ta taya ta murna sosai har da yi mata fatan Allah ya sa wannan shi ne mijin ta kuma ba ta shawara da ta riƙe shi da kyau har ta ƙara da faɗar “Duk namijin da zai iya kashe miki irin wannan kuɗi a ƙanƙanin lokaci ba tare da ya nemi wani abun banza a gunki ba to kar ki sake ya kuɓuce miki don kuwa irinsu suna da matuƙar wahalar samu a zamanin da muke ciki.”

Ta gamsu da zancen ƙawarta sosai ta yi mata godiya da fatan alheri ta koma gida.

A ɓangaren rayuwarta ta gida ma ta samu sassauci sosai musamman a ɓangaren mama da a yanzu take matuƙar ririta ta kamar za ta mayar da ita ciki.

Ranar farko da Surayyah ta fahimci ta fara samun ‘yanci a gidan, wata ranar Talata ce da misalin ƙarfe 11 na safe da ta fito da tulin kayan wankinta set sha biyar da zimmar wankewa. 

A can hanyar ƙofar gida ta saka kujera ta kusa da rariyar gidan saboda ta ji sauƙin zubar da ruwa kada ta ɓata gidan. Robobi masu faɗi guda biyu ta kwasa ta zuba ruwa rabi da rabi a cikinsu, sai ta suri bokitin fenti babba fari da za ta tara ruwa ciki ta ajiye don kada ta ɓata na cikin durom ɗin. Daidai lokacin Aishatu ta shigo gidan da irin bokitin a kanta cike da ruwa ta nufi wurin durom ɗin sai dai tun kafin ta zube idonta ya faɗa kan tarin aikin da yayarta ta fitar, a gaggauce ta zube ruwan ta ajiye bokitin tana kallon Surayyah.

Murya a sanyaye ta ce “Haba aunty! Don kin ga yau zagayena ne na ɗibar ruwa shi ne kika janyo wannan uban aikin?” 

Ganin kamar da lalama yarinyar ta yi zancen ya sa cikin taushin murya ta ce da ita. “Ba haka ba ne A’ishatu, mama ce ta ce na yi kawai ba komai tun da ina matuƙar buƙace da shi. Idan ya so idan suka ƙare sai mu sayi na kura.”

Ƙara matsowa kusa ta yi murya a sama ta ce “Tab! Wallahi kuwa ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa don ni ba jakar kowa ba ce, na fi son in zubar da ruwan nan a ƙasa da ki yi amfani da shi, ai wannan shi ne kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗin.” Rufe bakinta kedawuya ta kai hannu tana ƙoƙarin ƙwace ƙaramin bokitin da ke hannun Surayyah da nufin hana mata ci gaba da ɗibar ruwan wanda hakan ya yi daidai da shigowar Mama cikin gidan. “Me ke faruwa a nan ne? Ku fa shi kenan ba hali mutum ya ɗaga sai ya tarar kuna hatsaniya kamar wasu ‘ya’yan kaji?”

Ta yi zancen tana ƙarasowa inda suke ta tsaya a kansu. A’ishatu ce ta yi wuf ta ce “Mamanmu wai fa ruwan da na fi awa ɗaya ina fafutukar nemowa su ne za ta kwashe ta yi wanki don rashin imani. Shi ne don na yi mata magana ta ƙare mini zagi.”

Surayyah ba ta yi magana ba sai tsayawa da ta yi tana kallon ikon Allah da jiran ta ga  matakin da mama za ta ɗauka don ta sani a kowanne irin lokaci mama bayan A’ishatu kawai take bi imma ita ce da gaskiya ko akasin hakan sai dai ga mamakinta dai ta ji maman na faɗar “Ke A’ishatu ba na son rashin kunya, da sane na za ta yi, ni na ba ta dama. Ki sake bokitin kafin na mauje ki.”

Ba ki ta saki galala tana ci gaba da kallon maman har ba ta san lokacin da A’ishatu ta sake mata bokitin ba sai da ta ji nauyin shi ya ragu a hannunta kuma ya koma ƙasa sannan ta ɗago ido ta kalla.

Mama ta fara magana da muryar faɗa “Wai A’ishatu me ke damun ƙwaƙwalwarki ne? Na ga kwanakin nan rashin kunyar ki ta ƙaru, ita ba a gaba take da ke ba sosai? Ko don kin ga kafaɗarki ta kamo tata ne? To ita ma dai nan kusa za ta ɗaga ta bar miki gidan kamar yadda su Sadiya su ka yi kin ga ai sai ki nemi abokin yi. Ɓace daga gun nan kafin in tattaka ki fitsararriyar kawai maƙaryaciya.”

Sosai mamaki ya cika Surayyah wai ita mama ke goyon baya yau? Lallai duniya sabuwa abin dai yau sai ido wai bebiya ta auri makaɗi.

Da tana ta ƙoƙarin gano dalilin sauyin a ƙwaƙwalwarta sai yanzu ta samu amsarta a cikin kalaman maman. Kenan shigowar Ahmad a cikin rayuwarta ne ya kawo mata wannan hasken ‘yancin? Idan haka ne kuwa za ta ƙara riƙe shi da kyau domin ba za ta so ta rasa shi ba.

Aishatu da ta ga ba ta samu goyon baya ba sai ta wuce fuu tana zumɓura baki, baƙinciki kamar zai kar ta.

Washegarin ranar da dare Ahmad ya zo hira ya tsaya daga waje ya yi kiranta a waya ya sanar mata. Cikin zumuɗi ta shirya dama ta yi wankanta tun da yamma don haka kaya kawai ta sauya ta sanya hijabinta iya gwuiwa ta goga man leɓe ta goga turaren jiki mara ƙarfi sosai sai ta ɗauki darduma ƙatuwa ta fita.

Al’adarta kenan ba wai a kan iya Ahmad ba duka samari biyun da ta yi a baya idan sun zo hira ba ta yin kwaliyya ta zarta ƙa’ida ta fi son su san ta a asalin kalarta ta yadda mutum zai so ta a kowanne hali, haka nan ba ta ƙoƙarin ɓoye halayenta da ɗabi’unta ta zaɓi ka san ta a yadda take domin ka yi hukuncin ko za ka iya rayuwar aure da ita ba sai an shiga daga ciki ba idan lokaci ya bayyana zahirin halayyarta ba ka ɗauka ta yaudare ka ko zaman ya ƙi daɗi.

Ta sha ganin kyasa-kyasan aure da yawa da suka mutu a dalilin waɗannan abubuwan biyu shi ya sa ta ƙara dagewa kan nufinta domin gujewa shiga tsilla-tsilla bayan aure.

A ƙofar gida ta same shi ya jingina a jikin motarsa ƙirar Mazda 323 kalar ruwan siminti da fara’arta ta nufe shi “Assalamu alaikum, sannu da zuwa officer.”

Ya ɗago fuskarsa da murmushi yana amsawa da “Yauwa matar officer.” Sai dai kafin ma ya rufe bakinsa ta ga kalar kallon da yake yi mata ya sauya daga na farko.

Bayan sun gama gaisawa ta koma saman dandamalin gidansu ta yi shimfiɗa tana yi masa iso, bai ƙi ba ya ƙarasa kan shimfidar ya zauna sai dai tana lura da yanayinsa kamar yana cikin wata damuwa kasancewar akwai gulof ɗin lantarkin gidan da ke hannun riga da nasu yana haska musu fuskar juna.

Sun fi mintuna biyar a zaune shiru ba wanda ya yi magana, lokaci zuwa lokaci yakan  ɗago kansa sama ya kalli fuskarta sai kuma ya yi saurin janye idonsa ya mayar kan wayarsa ya ci gaba da shafawa. Ita kuwa da ta ji shirun ya yi yawa tana ta sauraren shi ba ta ji ko ta ga alamar zai yi magana ba ga shi kuma yau ta gan shi da yanayin da ba ta saba gani ba ya saka cikin damuwa ta kalle shi tana faɗar

“Darling me ye matsalar ne? Na ga kamar kana cikin damuwa.”

Bai yi magana ba dai har a lokacin sai ita ce ta sake cewa idan akwai wata matsalar ne ka sanar da ni, ba mamaki ina da shawarar da zan bayar da za ta yi amfani.

Jiki a sanyaye ya ɗago ya kalle ta suna haɗa ido ya yi hanzarin sunkuyar da kansa ƙasa bai ƙara ɗagowa ba, kan nasa a ƙasa ya ce “Ba komai, kawai dai yanzun nan na ji yanayina ya sauya ba kuma abin da aka mini.”

Za ta ƙara magana kenan ya tari numfashinta da faɗar “Kina ji, yanzu dai ki tashi ki shiga gida za mu yi magana anjima in sha Allahu. Ina zuwa jira ni.”

Bai  yarda sun sake haɗa ido ba ya nufi motar ya buɗe gidan baya ya ciro wata farar leda ya tako ya miƙa mata yana faɗar “Ga tsarabarki. Ni zan tafi.”

Duk da jikinta ya gama mutuwa da ganin yanayinsa amma hakan bai sa ta yi ƙasa a gwuiwa ba wurin faɗar “Don Allah ko za ka sauke ni nan Abuja road.”

Hannu ya saka a aljihu ya ciro kuɗi ya miƙa mata sai ma ta lura kamar hannunsa na rawa don har sai da dubu ɗayan da yake miƙa mata ta faɗi ƙasa kafin ta kai ga amsa.

Muryarsa da ɗan rawa yake faɗar “Ga wannan ki hau abin hawa ki ƙarasa ni zan tafi ina ujila.”

Sakanni ta share ƙame a gun cikin mamaki kafin ta sunkuya ta ɗauki kuɗin daidai lokacin da ya figi motarsa da sauri ya ɓace daga layin. 

Ciki ta koma ranta duk a jagule ba za ta iya sanin abin da ya ɓoye a zuciyarsa ba amma kamar ta lura a ɗan firgice yake yau. Kamar an canza mata Ahmad ɗinta domin kuwa Ahmad ɗinta mai yawan fara’a ne, mai wasa da dariya da son nuna mata soyayya da yawan zolayarta, amma yau ba ko ɗaya daga cikin ɗabi’un nasa da ta gani duka sun yi ɓatan dabo cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

Zuciyarta cike da wasi-wasi ta isa ciki tana ta saƙe-saƙe a ranta tare da fatan koma me ke damunsa Allah ya sauƙaƙa masa, Allah kuma ya sa matsalar ba daga ɓangarenta ba ne.

ƁANGAREN HALISA

Duƙar da ita ta yi ta kai mata uwar shirga a baya sai da ta gantsare ta ƙwallara ƙara sannan maman ta kama kunnenta ta murɗe da ƙarfi ta fara magana rai a ɓace “Wato ke ga mai kunnen ƙashi ko? Sau nawa ina yi miki nasiha a kan ki nutsu ki daina ballagazanci? Ba ki san kin shiga layin manya ba a yanzu?”

Ta sake mata kunnen tana ci gaba da faɗar “Yanzu kin shiga sahun manya kin fara dakon zunubi a karan kanki duk laifin da kika yi a kanki zai ƙare sai dai haƙƙi ne a kaina na faɗa miki gaskiya. Bar ganin kakarki ta ɗaure miki ƙugu wai ke ga taɓararriya renon kaka to ki sani raminki dabam nata dabam.”

Gefe Halisa ta samu ta maƙure tana matsar ƙwalla domin ta ji dundun ya shige ta da kyau, maman ba ta sakawa bakinta linzami ba ta ci gaba da faɗan.

“Wai tsabar rashin kan gado shi ne kike satar rake a baron mai ita, ƙarin neman a san ba ki da kunya ma shi ne kina tafe kan hanya kina sha har da cewa saurayi ya biya. Ke nan har ji kike kin isa kula samari?”

Sai a lokacin ta yi ƙoƙarin kare kanta cikin muryar kuka “Wallahi mama ko wane munafukin ne ya faɗa miki ƙarya yake yi mini. Abdul ba fa saurayina ba ne ɗan unguwarmu ne ya rage mini hanya.”

Cikinta maman ta yo gadan-gadan tana faɗar “Au Allah! Kenan dai bakinki ba zai mutu ba ko? To idan ni kin raina ni ki jira haɗuwarki da yayanku don na san dole sai ya ji labari.”

Turo baki ta yi gaba cikin shagwaɓaɓɓiyar murya “To ni dai ki yi haƙuri mama. Don Allah shi ma ki hana shi dukana.”

“Za ki gani ne idan zan hana shi.” Daga haka ta koma bakin aikinta ta ci gaba da yi, ita kuma Halisa ta koma ɗakin maman har ta kwanta ta miƙe ta yi ɗai-ɗai a ƙasa tana yan waƙe-waƙenta na indianci maman ta shigo ta fatattake ta da faɗar

“Irin wancan lalacin da kike yi a gidan kakarki ni ba za ki yi mini shi ba a nan. Ta shi za ki yi yanzu nan ga kayan Kausar nan da ta ɓata ki wanke mini su tas.”

Miƙewa ta yi zaune tana kallon maman wani irin kallo, ‘wanki kuma? Gaskiya da sake an gama rabo mai kaza ya tashi da kai.’

“Ai ba sai kin shiga dogon nazari ba, na ji a can ma wai ita innan har wanki take yi miki don ɗaurewa ƙarya ƙugu. Ke dai ba ‘yar kowa ba ‘yar galadiman tsumma wai ba za ki yi wanki ba. To idan kuma kika yi aure fa? Kin ga ai sai mu ga ta faɗi ƙwarƙwata ta kada ƙudan cizo.”

Ta ja uban tsaki ta yi waje, can bayan minti ɗaya sai ga ta ta dawo ta miƙawa Halisa kuɗin sabulu da omo ta karɓa ta fita tana ƙunƙuni a ranta take faɗar ‘Don dai ba yadda na iya ne wai jaki da kayan taiki.’

Ta san muhimmancin uwa tun da a islamiyyarsu ana yawan jaddada musu wannan ko a cikin nasihohin da ake musu na yay da kullum shi ya sa ba za ta tsaya yin musu ba saboda duk abin ta tana tsoron azabar Allah.

Yadda uwar ta tsara haka ta yi wannan karon da ta fita ta kama kanta ba ta tsokani kowa ba, sai dai da iya tafiyarta kawai za ka gane ba nutsuwa a tattare da ita. Haka ta dawo ta kama aikin da aka saka ta domin gaba da gabanta in ji aljani da ya taka wuta.

Kayan Kausar sun kai set goma tana cikin wankewa sai da ta yi rabi maman ta ƙaro mata da nata set biyar. Turo baki ta yi gaba ta coke kamar za ta harbo sama take ji amma ba dama, ba ta ga fuskar yin tsiwa ba ballantana wata taɓara. Ta ci gaba da wankin tana yi tana ‘yan gunani can ta jiyo sallamarsa a ƙofar gida. Ai da ƙarfin tsiya ta yi baya tana sakin kayan hannunta ta miƙe da nufin guduwa ta ɓuya daidai lokacin mahaifiyarsu ta fito daga lokon da take ajiye tarkacen kwanukanta ta nufo murhun nata riƙe da kwandon kwanukan a hannu ta ajiye ta yi hanyar ƙofar gidan don amsa masa sallama lokaci ɗaya kuma tana bankawa Halisa ƙatuwar hararar da take yi mata inkiya da kada ta yarda ta gusa daga gun.

To fah jama’a ga yaya (aradun Halisa) ya shigo gidan ko ya za ta kaya?

Surayyah fa me ke faruwa a ɓangarenta? Me ya janyo sauyawar Ahmad ya rikirkice a ƙanƙanin lokaci?

Ku tara da ni a shafi na gaba.

UMMU INTISAR CE

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here