PP 13
ƁANGAREN SURAYYAH
Washegari ta tashi da sauƙi da ma tun jiya da baba Mai tawada ya saka mata magani kunamar ta faɗi, inda Allah ya taimake ta kenan shi ya sa har ta iya fita ta yi duk abubuwan da ta yi a jiyan.
Ga kuma ƙarin taimako da magungunan da likita ya rubuta mata take sha suke yi a jikinta.
Da misalin ƙarfe bakwai na safe ta sauko daga kan gadon da ta kishingiɗa don ƙarasa baccin safe, ta kalli Innare da tuni ta tashi tana ‘yar dagwainiyarta a tsakankanin bango da bangon ɗakin. To dayake ta su tsofaffi ba ka iya raba su da wannan yawon na cikin ɗaki ko tsakar gida, sun riga da sun saba motsa jiki da ayyuka irin su daka, shiƙa, surfe da sauran su. Sai kuma ubangiji ya ara musu dogon rai suka rayu zuwa wannan zamanin da aka fara yin adabo da waɗancan ayyukan aka zamanantar da su, shi ya sa ba su da wani zaɓi yanzu da ya fi wannan ɗin, wannan ya sa ba ta damuwa don ta ga Innare na yin hakan.
“Innare za kuwa a samu wani abin taɓa wa a wajenki, wallahi yau yunwar safe ce ta sako ni a gaba?” Ta tambaya tana yin hamma da ba za ka iya rarrabe ta me ce ce ba a tsakanin bacci da yunwar, lokaci ɗaya kuma tana zuro kafafuwanta ƙasa da nufin saukowa.
Ta waiwayo ta kalle ta ta ɗauke kai zuwa duban wani ɓangare a ɗakin tana faɗar “Da ma haka kuka iya ‘ya’yan zamani, daga ci sai bacci. Sauko ga ɗumame can da waccan uwar taku shugabar ‘yan rawar kai ta aiko mini.”
Sarai ta gane wacce take nufi wato baaba Hanne, ita ce wacce ba su cika shiri da surukar tata ba saboda iya ɗibar albarkarta ga shi ba ta ganin kan kowa da gashi.
Murmushi kawai ta yi ta sauko ta ɗauko kwanon ta zauna tana faɗar “Kai Innare, ban san sai yaushe takun saƙar da ke tsakaninki da surukar ki zai ƙare ba.”
Sai da ta ɓantari goronta ta tauna kafin ta ce “Zai ƙare ne a lokacin da ta nemo mutuncin da ta rasa.”
Dariya kawai ta yi ba ta ƙara tamkawa waccen magana ba sai tambayar tsohuwar da ta yi ko za a rage mata abincin? Ta nuna ita ba za ta ci ba, wannan dalilin ya sa Surayyah ta ɗauki ƙullin man shanu ɗaya a cikin waɗan da Innare ke sayarwa ta zauna tana ci.
Wani kallo mara saiti Innare ta watsa mata “A kan wane dalili kika ɗaukar mini kayan sana’a?”
Ture farin ƙaramin bokitin da man ke ciki ta yi gefe tana faɗar “Bashi na ɗauka, zan biya daga baya.”
Innare ta kawo na gani ta saka mata ta riga ta san cewa wannan irin zubin adashin da ba ɗauka take yi don kuwa bashin da jikokinta ke ci a wurinta ba irin wanda ake biya ba ne, kyautar dole yake komawa amma dake tsohuwar tana da sanyin hali idan ba ka taɓa mata abu biyun nan ba, wato mutuncinta da kuma jikokinta, shi ya sa ma ba ta iya yin komai a kansu ko sun taɓa abinta.
Waɗannan dalilan ne a kodayaushe ke haɗa ta rigima da surukarta Hannatu saboda ita duka biyun ba wanda ta bari.
Sauran sarakanan nata duka suna iya ƙoƙarinsu wurin girmama ta da gujewa ɓacin ranta tare da yi mata biyayya amma ban da uwamu mai ido tsakiyar kai.
Hanyar fita waje ta kama tana ƙyarawa Surayyah zance cikin raha. “Ki ci gaba da ci, tara ki nake Allah ya kawo mijin aurenki duk sai ya biya ni kuɗaɗena.”
Sosai Surayyah ta yi dariya ba dai ta ce da taohuwar komai ba, tana kammala kimtsa cikinta ta miƙe ta gyarawa tsohuwar ciki da wajen ɗakinta tas ta share ko’ina.
Abin da ta al’adanta kenan muddin ta ci abinci ba ta kwanciya sai bayan mintuna goma don ya gama narkewa, haka nan ma ba ta shiga banɗaki sai bayan lokacin. Ta ji masana na faɗar hakan garkuwa ne da
ke yaƙar cututuka da yawa kuma yake hana tara tumbi, shi ya sa idan har ka ga tana kammala ci ta kwanta ko ta kewaya to babban uzuri ne da ita.
Ta shirya ta fito za ta tafi gida kenan ta ci karo da wata maƙociyarsu ta bayan layi ta shigo gidan ta kalle ta “A’ah hajiya Sury manya.”
Da fara’a Surayyah ta ce da ita “Ina kwana maman Najmah?”
Amsawa ta yi ba tare da ta ɗauke ido a kan Surayyar ba sai ita ce ta sake cewa “Yau ke ce gidan namu da sassafe?”
“Eh wallahi zan sayi daddawa ne da maggi ina fatan akwai.”
“To ba na ce babu ba, sai kin shiga ki gani.”
Maman Najmah ta sake cewa “Za ki je gida ne?” Wannan karon kai kawai ta gyaɗa don ta fara gundura da zancen.
“To Allah ya tsare ya kawo lokacin da ke ma za ki bar wannan yawon neman makwancin ki huta.”
Ta fuskanci magana matar ke son gwaɓa mata sai ka ce a kanta take zaune ta zuba mata idanu tana faɗar “Me kika ce?”
“A’a cewa na yi yaushe za ki yi aure ne mu sha biki?” Ta yi zancen tana dariyar da Surayyah ta rasa ta me za ta kira ta, yaƙe ce ko ƙeta?
Ba ta ɗauka abin zai yi mata zafi kamar yadda ta ji shi yana ƙona mata zuciya ba, har ta lallashi zuciyarta ta juya za ta fita sai ta ji kuma ba za ta iya ba ta waigo da sauri tana faɗar “Sai randa kika shirya aurar da ni maman Najmah. Duk ranar da kika gama kimtsawa kika samo mijin kawai ki sanar da ni. Ni Mai biyayya ce uwata.”
Daga haka ta sake juyawa zuciyarta na ƙuna ta fice daga gidan ba tare da ta saurari matar da ta ji tana ƙoƙarin kare kanta ba.
Tun kuma daga ranar ta yi alwashi a ranta duk wanda ya ƙara yi mata tambayar banza a kan aurenta tabbas zai samu amsar banza ko da a ruwan sanyi ne, ta jure abin da ta jure a baya yanzu ta fuskanci idan ba martani ta fara mayar wa ba zuciyarta za ta illata.
Ko da ta isa gida goman safe ta gota don zamanta ta yi gidan gandun nasu sai da ta tabbatar ta huta da kyau. A hakan ma saboda gudun mitar mama ne da ba za ta koma ba sai sha biyun rana tun da ba a tausaya mata sam.
Tana isa gidan ta shiga da sallamar ta, daga kitchen maman ta amsa sallamar sannan ta fito hannunta riƙe da babban farantin silba ta kalle ta “Ashe ma ke ce, sai yanzu kike dawowa?”
Ta janye idonta daga kallon maman “Eh mama, yau na yi nauyin bacci ne, ƙila har da jinyar da nake ma ta janyo hakan.” Ta faɗa tana wucewa ciki. Maman ta biyo bayanta tana faɗar “Hakan za ta iya faruwa, ya jikin naki to?”
“Da sauƙi ta amsa a taƙaice tana shigewa ɗakin mama ta zauna daga gefen kujera a bakin ƙofa. Ita kuwa maman komawa ta yi kan kujera ‘yar tsuguno da ta tashi ta zauna a kai tare da ɗaukar baƙar ledar da ke gefenta ta ɗora farantin a cinyarta tana yage ledar sai ga farin wake ya bayyana ta fara tsincewa can ta ɗago tana kallon cikin ɗakin da ke gefenta.
“Yauwa Surayyah ina so mu yi magana ta fahimta da ke.”
“To Mama ina jinki.” Ta tattara hankalinta ta mayar gun maman.
“Ɗazu Atika ta nan gabanmu ta zo wurina da zancenki.”
Lulawa nazari ta yi na ‘yan sakanni kafin ta ce “Wace Atikar mama ban gane ba?”
Mama ta dakata da aikin da take yi na ɗan lokaci tana faɗar “Haba mana Atika dai ta can gaban gidansu Jummai, matar nan fara mai ƙiba kin gane ta ko?”
Murmushi mai kama da dariya ta yi tana faɗar “Oh! Maman Salman za ki ce mini, na gane ta sosai ai ina da ƙawa a gidan nasu ma.”
“Yauwa, Allah ya bar ki ita fa. To ita ce ta zo mini da zancen cewa jiya da ƙaninta ya shigo inda take da rana ya ganki shi ne ya yi mata magana a kan don Allah ya na so ta nema masa izinin yin magana da ke domin shi dai ya ga matar aure.”
Shiru ta ɗan yi tare da yin ƙasa da kanta tana sauraren bugawar zuciyarta da ya ƙaru kaɗan-kaɗan sannan ta ce “To ita mama ya aka yi ta gane ni yake nufi?”
Mama ta ci gaba da aikin tsintar wakenta tana faɗar “Kin ji ki da wani zance kuma, ita Atikar ce ba ta sanki ba? To ba ma iya ke kaɗai ba bana ji kaf ‘yanmatan layin nan za ta kasa shaida su. Kwatance ya yi mata ta fahimta, ta gaya mini har hotonki ta saka aka nuna masa ya tabbatar ke ɗin ce. To ta faɗa mini ya ce zuwa ranar juma’a mai kamawa zai zo ku gana za ta shirya muku haɗuwa me kika ce?”
Shirun ta sake yi ba ta iya ɗago kanta ba har a lokacin, zuciyarta na yi mata wasi-wasi da ta rasa na me ne ne, amma ba ta son mama ta zargi cewa ita ke gudun auren don haka ta ce “Shi kenan mama, Allah ya kai mu ya zaɓa ma fi alheri.”
Sosai fuskar Mama Hadiza ta bayyanar da farinciki tsantsa da fara’arta ta amsa wa ‘yar tata da “Amin ya hayyu ya qayyum, haka nake son ji ‘yata. Shi kenan za ki iya tashi Allah ya miki albarka.”
Ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wurin furta amin ta miƙe ta yi cikin uwar ɗaka ta zauna a ƙasan gefen gado tana ta tunanin iska. Idan za ka yanka ta a lokacin ba ta san sahihin abin da take tunani ba, sai dai ta yi fata a ranta cewa Allah ya sa ƙarshen wahalarta ne ya zo.
Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta yi kunya. Kamar yadda suka alƙawarta wa juna haɗuwa ta hanyar musayar yawun magabatansu hakan ce ta kasance. A wannan ranar tun ƙarfe uku Mama Hadiza take takurawa Surayyah a kan ta shirya da wuri, sai dai ita uwar gayyar wata iriyar kasala take ji a wannan ranar haka ta yi ta nauyin jiki har uku da rabi kafin ta shiga wanka.
Magana kuwa mama ta yi fin cikin cokali kafin ta gama shiryawa cikin atamfarta kalar ruwan hoda da ratsin tsanwa a ciki, ɗinkin riga da siket sun zauna a jikinta sosai dirinta ya bayyana ta so ta saka hijabi a kai amma maman ta yi tsayin gwamin jaki a kan lallai sai mayafi za ta saka tun da ganin farko ne kuma ma ai neman aure ne ba wata sharholiya ba.
Ba yadda ta iya haka ta je ma’ajin tufafinta ta ciro gyalen kayan da takalmin da zai shiga da shi ta saka. Maman ta kalle ta da murmushi “Yauwa ko ke fa? Ai haka kin fi haskawa. Yi sauri ki je kada ya riga ki ƙarasowa.”
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce “To mama zan tafi ɗin yanzu.”
“To sai kin dawo.”
Sai kuma ta ga ta ja ta tsaya tana maimaita faɗar za ta tafi sai a lokacin ta gano dalilin dakacin da aka samu rashin yi mata addu’a da ta yi, kuma muddin ba ta yi ba ta tabbatar ba za ta ta fi ba, ita haka take.
Murmushi ta yi tana ƙara kallon ‘yar tata da soyayya “To Allah ya tsare ‘yar albarka, a gaishe mini da surukin nawa.”
A kunyace ta fice daga gidan lokacin bai fi saura minti goma huɗu ta yi ba ta nufi gidan Atikar a ranta tana ta mamakin sakin fuskar da take samu daga maman a ‘yan kwanakin nan.
Da murna Atikar ta tarbe ta sai wani nan nan take da ita. Ta tarar ta gama shirya musu komai ta gyara ɗakinta tsaf inda za su yi zaman tattaunawar sai zuba ƙamshi yake a nan ta zauna suna ɗan taɓa hira kafin Atikar ta fita yin wani uzuri.
Sai bayan mintuna goma sha biyar da zuwanta gidan ya ƙaraso, da sallamarsa ya shiga ciki yayar ta tarbe shi da murna tana faɗar “Sannu da zuwa gwauron ƙanina mai albarka.”
Ya yi ‘yar dariya yana ba ta amsa da “Na dai kusa fita daga wannan gorin naki ni ma.”
“Au ka ji haushi ne? To ka zuciya mana ka yi auren nan da wata ɗaya.”
Cikin raha ya ce “Na dai gano ki kina taya kucakar ƙanwarki kishi ne don na zaɓa mata kishiya ban zaɓe ta ba.”
Surayyah da ke ciki tana jiyo hirar tasu cikin fara’a muryar tana ƙara kusanto ɗakin da take ciki a zaune. Da sauri ta gyara zaman mayafinta ta ciro wayarta tana duba fuskarta ta glass ɗin wayar kenan ta jiyo sallamarsu ta yi hanzarin kife ta a cinyarta tana sunkuyar da kai.
Atikar ta tsaya a gefenta tana faɗar “To Surayyah ga ƙanina, ɗa ne a wurin kawuna yayan mahaifiyata kuma dai shi ne ɗan’uwa kuma ɗa ma fi soyuwa a danginmu saboda nagartarsa.”
“Kai kuma Ahmad ga ƙanwata Surayyah tana ɗaya daga cikin ‘yanmata ma fiya hankali a unguwar nan tamu da na sani.”
Tana gama gabatar musu da juna ta fice don ta ba su wuri su gaisa sannan ta haɗo musu abin taɓawa.
Shiru ya ratsa ɗakin na ‘yan daƙiƙu dukansu ba wanda ya yi kyakkyawan motsi sai can dai ya katse musu shirun ta hanyar yin gyaran murya yana ƙure ta da ido ya ce “Amincin Allah ya tabbata a gare ki kyakkyawa.”
“Amin tare da kai.” Ta furta ba tare da ta ɗago kanta ba.
“Da za ki yi mini alfarma ki ba ni damar kallon kyakkyawar fuskarki mai ɗaukar hankali da jefa nutsuwa a zukata da zan fi jin daɗin hakan don na gabatar da kaina.”
Sannu a hankali ta ɗago kai ta zuba masa matsakaitan idanunta da suke ɗauke da ƙwayar ido fara tatas mai ƙyallin ɗaukar hankalin mazaje.
Ummu Intisar ce




