Home Siyasa Na fita daga jam’iyyar APC ne saboda ba a ƙaunata—Honarabul Ambarura

Na fita daga jam’iyyar APC ne saboda ba a ƙaunata—Honarabul Ambarura

10
0

Ɗan majalisar waƙillan Nijeriya dake waƙiltar ƙananan hukumomin Gwadabawa da Illela Honarabul Bello Isa Ambarura ya fice daga jam’iyyar APC ya koma jam’iyyar adawa ta ADC tare da magoya bayansa.

Isah Ambarura ya bayyana ficewarsa a Talata bayan kammala taro da magoya bayansa a birnin Sakkwato ya ce sun bar jam’iyyar ne saboda ba a ƙaunarsu.

“Dole ce ta sanya muka bar jam’iyyar APC muka shiga ADC tun da mun gano ba a ƙaunar mu,” a cewarsa.

Honarabul Ambarura ya daɗe yana takon saƙa da jagororin jam’iyyar APC a jihar in da ya ƙauracewa duk wani taron su da yin hulɗa ta siyasa.

Yanayin siyasa ya fara zafi a jihar Sakkwato in da ake ganin jam’iyyar adawa ta ADC na iya yin ƙarfin da za ta zama barazana ga APC a jiha in da a yanzu ta samu ƙarin magoya baya, Sanata Ibrahim Lamiɗo da yake waƙiltar yankin Sakkwato ta Gabas tare da magoya bayansa sun shiga jam’iyyar don kasa magance tsaro da gwamnatin APC ta yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here