Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 11

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 11

3
0

ƘADDARA TA RIGA FATA

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

MAMAN ABDALLAH, MAMAN BASH, SA’EEDA SADIYA NA GASKIYA FANS D, WANNAN SHAFIN NAKU NE, DOMIN TUKWAICIN IRIN ZAFAFAN COMMENT DA NAKE GANIN KUNA MUN AKAN WANNAN NOVEL, NAGODE ALLAH YA BAR MU TARE, IDAN BA KU BABU BOOK.

SHAFI NA 11📑

__📖 Tun da na idar da sallan ban tashi a wurin ba, har lokacin ishaa yayi na tashi na fara yin sallan, ina cikin yin shafa’i da wutiri naji ana shigowa cikin ɗakin, ina cikin sujuda naji muryan su Abbu da Ummi, suna gaisawa da Amal, daga baya kuma naji Dr Abdallah ya musu sallama ya bar ɗakin.

Ina idar wa na juyo fuska na ɗauke da murmushi ina gaishe su, kaman wanda muka shekara da sanin juna mu kayi ta hira da su, in da Ummi ke bani labarin ciwon Amal da yadda yake ba ta wahala,

“yaran mu uku a duniya, babban Yayan Amal wanda shi tun yana ƙarami Allah ya mishi rasuwa, kuma shi sai ya kasan ce, AA, sai mai bi mishi shi kuma AS ne, yana karatu yanzu haka a Oxford university, mai suna Faisal yana shekaran shi na ƙarshe kenan, in da ya ke karantar medicine, Amal ita ce mace a cikin su, kuma ita Allah ya ɗaura mata wannan laluran, amma kuma mungode Allah da ya bamu juriya da haƙuri na kula da ita, saboda shi ciwo ne wanda mai ciwon da mai jinyan kullum a wahale suke, mun so tayi karatu a kusa da mu cewar Ummi, amma sai nayi tunanin wata rana fa Amal in tana da nisan kwana, za tayi aure kuma bamu san in da auren zai kaita ba, shiyasa muka yanke shawaran kawota nan tayi karatu, amma kullum a cinkin fargaban ciwon ta muke”.

Ummi ta faɗa tana ta daddanawa Amal ƙafa, wanda tun shigowan ta abinda ta ke tayi mata kenan.

Haka mu kayi ta hira har Dr Hussain ya shigo, gaisuwa ya musu na girmamawa, wanda daga gani Abbu yaji daɗin hakan, haka ina lura da Abbu sai jan Dr da hira ya ke tayi, shi kuma cikin kunya da rashin sabo da yawan magana ya ke amsa mishi.

Muna ta hira ni da Ummi akan karatun mu, ita kuma Amal ta rufe idon ta kaman mai bacci, amma idon ta biyu don wani lokacin ta kan buɗe idon ta tana amsa mana wani maganan, wani kuma tayi shiru tana kallon mu, ko kuma ta rufe idon ta, ita kaɗai tasan irin azaban da ta ke ji a cikin ƙasusuwan ta, sai kuma ƴan uwan ta masu irin wannan lalura.

ALLAH YA YAYEWA DUK WANI MAI CUTAN SICKLER NA DUNIYA, ALLAH KA SASSAUTA MUSU

Dr Abdallah ne ya shigo fuskan shi ɗauke da murmushi yana duban Abbu cikin yaren su na larabci yace,

“Abbu lokacin cin abincin Amal yayi, mai kula da ita zata shigo, sannan a ƙa’ida ba asan visitors a ɗakin, ko zan kai ku masauƙi ne Abbu”.
Ya faɗa yana bin Abbun da kallo fuskan shi yana ta fitar da murmushin da baya barin fuskar shi.

“Ba sai ka nema musu wurin kwana ba, ina ga kaman babu takura idan sun kwana a gidan Humaira ko gidan Amal”.
Dr Hussain ya faɗa ba tare da ya dubi idon kowa ba.

Murmushi Dr Abdallah yayi sannan ya dubi Abbu wannan karon cikin kalmar turanci, don yayi matuƙar mamaki da yaji Dr Hussain yana jin larabci yace,
“Abbu zaku iya zama a gidan Humairan ko na Amal ɗin?”.

“Nikan ina ga idan babu ta kura kuzo gida na kawai Ummi, saboda akwai extra room wanda Daddy ma anan ya zauna, ina ga zaku iya zama da Abbu idan bazan takura ku ba”.
na faɗa ina matsawa kusa da Amal ina riƙe hannun ta.

“Babu komai Humairah wurin ki dana Amal ai duk ɗaya ne, so babu komai zamuje gidan ki, tunda 2days ma kawai zamuyi mu juya, saboda munga jikin Amal ɗin Alhamdulillah, bai yi mata tsanani ba sosai”.
Abbu ya faɗa yana shafa kan Amal ɗin, wanda tun da taji maganan tafiyan mu ta buɗe ido tana bin mu da kallo ɗaya bayan ɗaya.

A hankali ta buɗe baki tace, “Ummi kuje gidan Humairah zata baku kula sama da yadda zan baku, kuma Hummy bata da problem, za kuji daɗin zama da ita sosai”.
ta faɗa hannun ta riƙe dana Ummin.

Haka muka yi sallama muka fita, muna zaune nida Dr Hussain a mota muna jiran fitowan su Abbu, don a ciki muka bar su saboda suyi sallama da ƴar su, bayan shima Dr Abdallah shima ya bar ɗakin.

“Me kika shirya musu for break fast”? Dr ya tambayeni ba tare da ya kalle ni ba.

Kallon shi nayi na kawar da kaina gefe ina kallon hanyar fitowa daga asibitin nace,

“ina ga ai chips is okay, sai na sayi bread su sha da tea, saboda larabawa basu wasa da cin bread”.
na faɗa ina juyowa ina kallon shi.

“Kina da enough potatoe ɗin?”.
Ɗaga mishi kai nayi alaman ehh, saboda ganin tahowan su Abbu.

“Idan babu na kira wife ɗina ta musu acan, idan yaso da safe sai na karɓo da sauri”.
ya faɗa yana wani munafukin murmushi, kallon shi kawai nayi bance mishi komai ba, saboda ganin su Abbu suna shirin buɗe ƙofan motan.

Haka muka yi ta tafiya kowannen mu bakin shi shiru, sai Ummi da Abbu da ke zaune a baya ne kawai suke magana, in da daga baya Abbu yake tambayan Dr ya ya za’ayi da maganan school ɗin Amal? Tun da gashi gobe monday ita kuma tana asibita, ya ya za’ayi kenan”?

Yana shiga gate ɗin gidan mu ya amsawa Abbu da cewa,
“gobe insha’Allahu zan yi report a school, duk abinda akayi tunda bata nan sai ƙawarta ta nuna mata daga baya, tunda ba laifi suna maida hankali akan karatun, so abin bazai musu wuya ba, sai dai addu’an Allah yasa kada abin ya ɗau lokaci”.

“Ameen ya rabbi”.
Abbu da Ummi suka amsa mishi.

Gidana na buɗe musu suka shiga, muna shiga suka zauna a parlor, ni kuma na shiga ɗaki domin na shimfiɗa musu bedsheet, domin tun da Daddy ya tafi na cire, sai dai bayan 2dys ina sha re wurin na goge komai, don ni ban yadda da zama cikin ƙazan ta ba, ina ta tunanin mai zan fito na ɗaura musu mai sauƙi for dinner.

Ina fitowa na dube su ina murmushi nace, “Ummi ko za kuyi wanka kafin na girka mana abinda zamu ci?”.
Na faɗa ina ƙarasuwa parlon.

“My luv kada ki wahalar da kan ki, kawai tea za musha da bread, saboda Abbun ko baya iya zama babu tea”.
Ummi ta faɗa tana miƙewa tsaye tana dariya.

Shima dariyan ya yi yana miƙewa yace, “Faɗi gaskiya dai, kice bamu iya zama babu tea daga ni har ke”.

Ni dai dariyan su kawai na keyi domin kaman basu suka haifi su Amal ba, babu wani girman kai ko raini suna wasa da junan su kaman ƙawaye, suna shigewa na ɗauki waya na da yake neman a ɗauke shi, domin ringing ɗin da yake yi.

“Ki fito waje ina jiran ki”.
cewar Dr Hussain, ajiye wayan nayi bayan naji ya katse ta shi.

Ina fita nagan shi tsaye a jikin motan shi, na ƙarasa wurin ya miƙo mun wani babban laida, mai ɗauke da tambarin MCDOULS take away yai mana, sannan ya miƙo mun ɗayan leda wanda yake cike da bread da wasu snacks ɗin kala-kala, ɗagowa na yi ina duban shi.

“Kinsan larabawa da son kayan flour, saboda haka ki shiga musu da shi, ni kuma bari na shigo da Potatoe ɗin da kuma plantain da egg, na ƙaro miki ne saboda kada ku takura”.

Hararan shi na yi cikin wasa nace, “hala matar ka bata iya soyawa ba ko? Shiyasa ta koro ka da shi kadawo min, dama dai nima nayi tunanin matar da ta ƙware da barin mijin ta da yunwa yana bin gidajen cin abinci? To yaushe tasan tayiwa baƙi idan ba neman magana irin na mazaje ba”.

na faɗa ina ƙarasawa balcony ɗi na, wanda shima yana biye da ni abaya yana ta murmushi bai ce mun uffan ba.

Har kitchen ya raka ni da kayan hannun shi, nima ajiyewa nayi na miƙe ina kallon shi ganin yadda ya ƙura mun ido bayan ya ajiye kayan hannun shi.

Murguɗa mishi baki nayi na juya ina ɗaga eggs ɗin ina saka su a wurin dana ke ajiyewa, sannan na zuba potatoe ɗin a cikin wani standing storage na zuba dankali da onioun,

“to ai sai ka tafi tun da ka gama aikin ka”.
na faɗa ina kallon shi nima.

Murmushi ya yi yace, “kin fara raina ni ko? Ni ba Malamin ki bane?”.

“Kuma Baby na ba, sannan kuma friend ɗina, kuma…. “.
sai nayi shiru ina kallon yadda ya ƙura mun ido.

“Kuma ɗan aiken ki ko?”.
Ya tambaya yana ɗaga mun giran shi sama, alaman tambaya da son jin ƙarin bayani.

Dariya na yi nace, “ni idan ba sharri ba yaushe na taɓa aiken ka?”.

“Gashi yanzu kin fitar dani naje miki aika, saboda kina ganin kin taddo ni tsayi ko”.

Matsowa nayi kusa da shi ina dariya nace,

“kaiiii wlh duk tsayi na ban fi zuwa ƙirjin ka ba, kaifa dogon gaske ne Dr’n mu, don ina mamakin mai ya haɗa ka da mata wanda bata wuce kwandon wanke-wanke ba a tsayi”.
Na faɗa ina dariya ƙasa-ƙasa.

“Yayan mu ina mamakin mai yasa ka ke son wannan corper? Wallahi kai dogo ne sosai gara kasamu mata doguwa, amma wannan corper kam ai bata wuce tsayin ragon da aka yanka na layyan bana ba, ƴar ƙuƙur kenan”.
cewar Aisha lokacin da ta rutsa ni a kitchen tana mitan neman corper da na ke yi.

Kallon Humaira na yi sannan na bata irin amsan dana bawa Aisha a wancan lokacin, wanda shi ne kawai nasan zai sa ka ta rufe bakin ta,

“to ke bakiga irin kyaun da ta ke da shi bane? Ina ruwa na da wani tsayin ta tun da ni ina dashi ai ya ishe mu, kawai kyaunta da yasa bana iya ganin na kowacce mace ne ya ɗibe ni na aure ta, kuma har yau bana ganin wacce ta fita a ido na, kowa ganin ta na ke yi kaman biri a gaba na don muni”.
ya faɗa yana wani jujjuya kanshi alaman abin ya mishi daɗi.

Fita nayi daga kitchen ɗin ban ko bi ta kanshi ba, wucewa ɗaki na kawai nayi don ganin su Abbu basu fito ba.

Ina wucewa ya yi dariya shi kaɗai yana tuna Aisha wanda lokacin ita tsabar haushi kuka ta fashe da shi taje tana gaya wa Ummi wai nace tana kama da biri, wanda Ummi ta ƙira ni tana cewa,
“saboda Allah Hussain ko wani kaji ya cewa ƙanwar ka tana kama da biri ai sai in da ƙarfin ka ya ƙare, ko dan Albarkacin ita tayi kamanni na ai za ka ce tafi kowa kyau a duniya”.

Hassan ne ya amsa da wuri yana cewa, “Ummi to wai ita meya sa ta damu da sai Hussain yace tana da kyau? Saunawa ina gaya mata kafin a samu mai kyaun ta sai antona, saboda kaf zuri’ar mu babu mai kyaun ta, amma nawa baya burgeta sai na amininta ta ke jira ya faɗa, wanda har ta mutu bazai faɗa ba, kuma ta haɗu da aiki wallahi, garama ta haƙura mijin auren ta wataran zai gaya mata”.

Hararan shi Aisha ta yi tace, “kafin nayi auren miji na yace ina da kyau, Yaya Hussain ɗin nake so yace ina da kyau, ai kai na gajji da faɗan da ka ke yi na shi kaɗai na keso ya faɗa, tun da shi ai bai taɓa faɗa ba”.

sannan ta kalli Ummi tace, “Ummi nah don Allah kice mishi ya faɗa mun ko sau ɗaya ne”.
ta faɗa tana kwanciya a jikin Ummin.

Ummi ce ta dube ni da faɗa tace, “bana wasa da kai Hussain kazo kagayawa ƴar uwar ka tafi kowa kyau a cikin matan duniyan nan, idan kana so mu zauna lafiya da kai yau a gidan nan”.

Dariya na yi har ina buga ƙafa na, muka tafa da Hassan sannan nace,
“Allah Ummi bazan faɗawa wata mace tana da kyau ba har sai matar da zan aura, ita ma kuma har sai ta shigo gida na zan gaya mata, domin zai fi mata daɗi, amma haka kawai na ƙarasar da kalma mai girma da daraja tun a waje? Lokacin da ya kamata na faɗa kuma ya zama bai mata daɗi ba? Gaskiya Ummi na ma gudu”.

da gudu na fita a ɗakin Ummi, wanda ina jin dariyan Hassan kaman zai tada Parlon ita kuma Aisha sai kuka ta ke tayi, Ummi na bata haƙuri.

Fita ya yi a kitchen ɗin cikin jimamin rashin familyn shi da ya yi na shekaru da dama a tare da shi? Ko ya ya Ummi ta ke? Ya ya Hassan zai ji idan ya buɗi ido bai ganshi ba a rayuwar shi? Duk da suna yawan faɗa amma suna son junan su wanda babu wanda ya ke shiga tsakanin su, don ko suna faɗa idan wani ya saka baki to sun daina, sai dai su rungume junan su suna dariya, kuma ko ya ya Aisha ta ke? Ko yanzu yaran ta nawa? Wata aura? Allah sarki Abban su ko ya ya zai ji idan babu ni a rayuwar shi? Duk da sun kasance ƴan biyu amma Abba yafi nunawa Hussain soyayya, Allah sarki Aunty Hauwa ita kam yasan hala sai tafi Ummi shiga damuwa.

Har ya shiga part ɗin shi hankalin shi a tashe, yarasa me yasa tun haɗuwar shi da Hummy ya zama kullum suka haɗu sai ta tuna mishi da wani abu na familyn shi.

Kwanciya ya yi a parlor, sannan ya ƙira ni, ina ɗauka muryan shi a hankali yace,
“Babyn baby na tafi don Allah ki bawa baƙin nan abincin, naga kin wuce ɗaki bamuyi sallama ba”.

“Naji yanzu ma ina kitchen ɗinne, gudnyt”.
na faɗa mishi ina kashe wayan, don har yanzu raina a ɓace ya ke da shi.

#Comment & Share.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here