Sakkwatawa suna jinjina ga Gwamna Ahmad Aliyu kan aiyukkan raya karkara—Bajare
Mai baiwa Gwamna shawara kan hanyoyin karkara(tituna) Malami Muhammad Galadanchi wanda an ka fi sani da Bajare ya yabawa Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto kan bunƙasa hanyoyin karkara da ya yi fiye da Gwamnatin da ta gabata, wanda hakan ya sanya Sakkwatawa ke jinjina gare shi.
Bajare a hirar sa da Managarciya kan shekarru uku na gwamnati Ahmad Aliyu ya ce Sakkwatawa sun dace da samun gwamna wanda ya ke kula da yanayin da suke ciki da zimmar ciyar da jihar gaba a fannoni da dama na rayuwar yau da kullum.
“Gwamnatin nan ta Dakta Ahmad Aliyu tun da ta fara jan karagar mulki shekarru uku da suka gabata ta samu hanyoyin karkara a dukkan ƙananan hukumomin jiha cikin mawuyacin yanayi wasu ba a iya bi saboda yashi, wasu idan Damana ta zo shikenan ruwa za su mamaye su, ba halin a hau sai dai a zagaya tafiyar minti 30 ta koma ta awa uku zuwa biyar a haka ake ta fama.
“Gwamna saboda kishinsa ga jama’arsa musamman na karkara nan take ya duba hanyoyin da aka fi buƙatar samuwarsu ya ba da umarnin soma aikinsu nan take, a haka ya tsara a hankali ya ƙudurci zai gyara duk wata hanya ta karkara da ta shiga cikin wani yanayi marar kyau, zai kuma samar da sabbi da za su sauƙaƙa harkar zirga-zirga tsakanin birni da karkara.
“Gwamnan talakawa ya aminta da samar da hanyoyin mota na bunƙasa tattalin arzikin jiha kan haka a birnin da karkara hanyoyi ake yi da yawan mutane lissafi ya ƙwace masu na adadin yawan hanyoyin da Gwamnatin Ahmad Aliyu ta samar a jihar nan,” a cewarsa.
Bajare ya bayyana a yanzu sun kammala hanyoyi da dama tsakanin waɗanda aka sanya ma kwalta ‘yar lumui-lumui (downloap) da kuma mai kwalta, da za su kai 55, kuma ba a tsaya ba, waɗanda ake yi a halin yanzu da ba a kammala ba, ɗan kwangila baya bin bashin ko Naira an biya shi, aiki kawai ake jiran ya kammala.
“Ba wani ɗan kwangila da muka baiwa aikin hanya da yake bin wasu kuɗin aiki, duk wani tsaikon aiki da za a samu bana kuɗi ba ne don mun biya dukkan masu aikin, nan da ɗan lokaci kaɗan za a kammala gaba ɗaya hanyoyin dake ƙarƙashin kulawar mu, da wannan nake cewa Sakkwatawa sun godewa Amadun Alu”.






