Home Rahoto Mahaifiyar da Gwamnan Kano ya yi wa ɗanta alƙawarin kai shi asibitin...

Mahaifiyar da Gwamnan Kano ya yi wa ɗanta alƙawarin kai shi asibitin Zuciya a Turai ta koka

26
0

Gwamna Abba Ya Hana kamfanin MTN Kai Al’amin mai Ciwon zuciya zuwa Ƙasar Waje, Amma Sama Da Shekara Ɗaya Har Yanzu Bai Cika Alkawari Ba — Mahaifiyar Yaro Ta Roƙi Gwamna Abba ya cika alƙawari tunda Ya hana MTN taimaka masu.

A kano Mahaifiyar wani yaro mai suna Al’amin, wanda ke fama da matsalar ciwon zuciya da Spinal Cord, ta roƙi Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya cika alkawarin da ya yi na ɗaukar nauyin kai ɗanta ƙasar waje domin yi masa aikin da zai taimaka wajen ceto rayuwarsa.

Fiye da shekara guda da ta gabata ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci Asibitin Yara da ke Zoo Road a Kano, inda ya haɗu da Al’amin da ke fama da matsalar lafiya.

A lokacin ziyarar, an ce kamfanin MTN ya shirya ɗaukar nauyin kai yaron ƙasar waje a cikin sati biyu domin samun kulawar lafiya, sai dai Gwamna Abba ya ƙi amincewa da hakan, inda ya bayyana cewa shi da kansa zai ɗauki nauyin jinyar yaron tare da kai shi ƙasar waje domin yi masa aiki.

Sai dai sama da shekara guda bayan wannan alkawari, har yanzu ba a kai Al’amin ƙasar waje ba domin samun aikin da aka yi masa alkawari.

Wannan lamari ya sake bayyana ne bayan an hango mahaifiyar Al’amin tana roƙon Gwamnan, tana neman ya tuna da alkawarin da ya ɗauka tun lokacin da ya ziyarci asibitin.

Mahaifiyar yaron ta yi kira ga Gwamna Abba da ya taimaka ya cika alkawarin da ya yi, domin halin da ɗanta ke ciki na buƙatar kulawa cikin gaggawa.

Abin da ya jawo hankalin jama’a shi ne yadda aka hana MTN ɗaukar nauyin jinyar yaron, yayin da sama da shekara guda bayan nan har yanzu alkawarin da Gwamnan ya yi bai samu cikawa ba.

Mahaifiyar Al’amin na ci gaba da fatan cewa Gwamnan zai saurari kukanta, ya cika alkawarin da ya yi, domin a kai ɗanta ƙasar waje ya samu kulawar da yake buƙata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here