Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam ya zama ɗan takarar gwamna a jam’iyyar adawa ta NDC a jihar ta Kano gabanin zaɓen 2027.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa shi ma mataimakin gwamna a jihar, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya samu tikitin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.
Tun da fari dai Gawuna ya ƙi karɓar tayin tikitin sanatan, inda rahotanni su ka ce daga baya kuma bayan tuntubar da shawarwari daga abokan siyasar sa, sai ya amince da takarar ta Sanatan.
A wani faifen bidiyo da Saifullahi Hassan, hadimi na musamman ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya wallafa, an ga jagoran Kwankwasiyya din na kira ga magoya bayan Kwankwasiyya da su fito domin tabbatar da takara ta Kwamared da Gawuna da kuma Peter Obi a jihar Kano a yau Juma’a.
