Home Siyasa Kotun Daukaka Kara  Ta Soke  Zaben Sanatan Zamfara

Kotun Daukaka Kara  Ta Soke  Zaben Sanatan Zamfara

19
0

Kotun Daukaka Kara  Ta Soke  Zaben Sanatan Zamfara
Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar da Sanata Sahabi Ya’u Kaura ya shigar domin ƙalubalantar hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau. Sanata Sahabi ya daukaka kara ne domin kalubalantar hukuncin soke zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta tabbatar da hukuncin baya  a shari’ar da Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, mai neman tikitin takarar sanata a APC, ya shigar.
Bayan tabbatar da hukuncin, kotun wacce ke zamanta a Sakkwato ta kuma tabbatar da umarnin gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani a wannan yanki. Lauyan Shinkafi, Bello Galadi, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan yanke hukuncin. Ya ce kotun ta warware dukkan batutuwan da Sanata Sahabi Kaura ya gabatar, sannan ta yi watsi da ƙarar saboda rashin cancanta. Bello Galadi ya ce sanatan ya ƙalubalanci hurumin Babbar Kotun Tarayya na sauraron ƙarar, amma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da ikon ƙaramar kotun na sauraron shari’ar da yanke hukunci a kanta. 
Ya ƙara da cewa kotun daukaka kara ta kuma yi watsi da hujjar cewa ƙaramar kotun ta yi kuskure wajen ɗora wa wanda ya shigar da ƙarar nauyin tabbatar da hujjoji.
A cewarsa, hujjojin da aka gabatar sun tabbatar da rashin bin ƙa’idoji da dokokin APC da suka tsara yadda ya kamata a gudanar da zaɓen fidda gwani.

Lauyan ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga dimokuraɗiyya da bin doka, yana mai cewa ya sake tabbatar da cewa babu wani mutum da ya fi ƙarfin doka. “Wannan hukunci ya tabbatar da cewa matakin da wanda nake wakilta ya ɗauka na tafiya neman hakkinsa a kotu ya dace, kuma ya aika da saƙo mai ƙarfi ga waɗanda suke ganin sun fi ƙarfin doka,” in ji Bello Galadi. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here