Home Manyan Labaru Matsalar Tsaro ta kara ta’azara a wata ƙaramar hukuma Gwamnan Kebbi ya...

Matsalar Tsaro ta kara ta’azara a wata ƙaramar hukuma Gwamnan Kebbi ya kai ziyarar jajantawa

23
0

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris Kauran Gwandu, ya ziyarci al’ummar Tsamiya da ke Karamar Hukumar Bagudo domin jajanta musu kan hare-haren ’yan bindiga da aka kai wasu sassan yankin.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Mai Bai wa Gwamnan Jihar Kebbi Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Yahaya Sarki, ya fitar.

Sanarwar ta ce gwamnan ya yi Allah wadai da hare-haren, tare da bayyana cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakan magance matsalar tsaro kuma za ta ci gaba da aiki da hukumomin tsaro domin kare al’umma.

Gwamnan ya ce ya zaɓi zuwa yankin da kansa domin jajanta wa al’ummar maimakon tura tawaga.

A yayin ziyarar, Hakimi Muhammadu Wankai ya nemi gwamnatin jihar ta duba yiwuwar gyara hanyar Kaoje zuwa Illo zuwa Lolo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here