Home Daga Marubutanmu KA YABI MATAR KA IDAN TA YI ADO: TARE DA KALMAR DA...

KA YABI MATAR KA IDAN TA YI ADO: TARE DA KALMAR DA ZA TA IYA ƘARA GINA SOYAYYARKU

32
0

KA YABI MATAR KA IDAN TA YI ADO: TARE DA KALMAR DA ZA TA IYA ƘARA GINA SOYAYYARKU

Shin ka taɓa tsayawa ka yi tunanin irin farin cikin da matarka take ji idan ta yi ado, ta shirya cikin kyakkyawar shiga, ta gyara kanta, sannan ta zo gabanka taji kalamai masu daɗi?
Abin takaici, wasu mazan suna kallon matansu cikin sabon shiga, amma su kasa furta ko kalma ɗaya ta yabo. Wasu ma har matansu sai sun tambaya, “Na yi kyau kuwa?” kafin su ji wata kalma daga bakin mazajensu. A wasu lokutan ma, sai dai su yi shiru kamar ba su lura da wani canji ba.
Ya kamata maza su fahimci cewa yabo ba wani abu ne mai wahala ba, kuma ba yana nufin mutum ya rasa kamun kai ba ne. Yabo wata hanya ce ta nuna ƙauna, kulawa da jin daɗin.
Mace tana iya ɗaukar lokaci tana zaɓen tufafi, kayan gyaran gashinta, da dai sauransu ba don komai ba sai domin ta burge mijinta. 
Ba lallai sai ka sayo mata kaya masu tsada ba kafin ka nuna mata cewa tana da kyau a idanunka. Wani lokaci kalmomi kaɗan kamar, “Masha Allah, kin yi kyau sosai,” “Wannan shigar ta yi miki kyau,” ko “Ina son yadda kike kula da kanki,” suna iya zama sanadin farin cikin da ba za ka iya auna shi ba.
Maza, ku fahimci cewa mace ba ta buƙatar kuɗi kawai daga gare ku, tana buƙatar kulawa ta fuskar magana da mu’amala.
Kada ka bari wasu mutane su riƙa yabon matarka, har su kai da suna lura da kyawunta, alhali kai da kake da damar nuna mata irin wannan kulawa kana nuna halin ko-in-kula.
Ka tuna, idan matarka ta saba samun yabo da kyakkyawar magana daga gare ka, hakan na iya ƙara mata kwarin gwiwar kasancewa kyakkyawa a idanunka. Haka kuma yana ƙarfafa kusanci da soyayya a tsakaninku.
Wasu mazan suna ganin yabo zai sa mace ta yi girman kai ko ta ɗauki kanta fiye da kima. Wannan fahimta sam ba haka ba ne. Yabo na gaskiya ba ya lalata mace; a mafi yawan lokuta yana sa ta ji ana darajjata ne.
Haka kuma, ba wai yabon ado kawai ake nufi ba. Ka yaba mata idan ta yi ƙoƙari wajen kula da gida, idan ta yi wani abu da ya faranta maka rai, ko tayi wani abu mai kyau. Kada kalamanka su kasance na kushewa kawai, har ma sanya ta fara tunanin cewa babu abin da take yi da zai taɓa gamsar da kai.
Ka zama mijin da matarsa ba za ta riƙa neman yabon wasu domin jin cewa tana da kyau ba, saboda tun a gidanta take samun kalaman da ke faranta mata rai.
A wannan gaɓar ina son tunatar da ƴan uwa maza cewa kyakkyawar rayuwar aure ba ta ginuwa da ciyarwa da tufatarwa kawai. Tana buƙatar kalaman ƙauna, yabo, tausayi da kulawa. Kada ka raina ƙarfin kalma mai daɗi a cikin zuciyar matarka.
Wataƙila abin da kake ɗauka ƙaramin abu ne, a gare ta ya kasance yana da babban matsayi.
Miji, idan matarka ta yi ado, ka dube ta da idon ƙauna, ka yaba mata da zuciya ɗaya. Kada ka bari shiru ya zama amsar da take samu a duk lokacin da ta yi ƙoƙarin faranta maka rai.

#Managarciya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here