Home Labarai Jingir: Kano Ba Ta Goyon Bayan kalaman da za su kawo rashin...

Jingir: Kano Ba Ta Goyon Bayan kalaman da za su kawo rashin lafiya da Rarrabuwar Kan al’umma—Kwankwaso

23
0

Kwankwaso Ya Yi Allah-Wadai da Kalaman Sheikh Jingir, Ya Ce Kano Ba Ta Goyon Bayan kalaman da za su kawo rashin lafiya da Rarrabuwar Kan al’umma ba.

Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran siyasa ɗan takarar Mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana matukar damuwarsa kan kalaman da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi a wani taro a Kano a karshen mako.

Kwankwaso ya ce a wannan lokaci mai muhimmanci da Najeriya ke ciki, ya kamata a yi Allah-wadai da duk wasu kalamai da ke ingiza rarrabuwar kai da rashin hadin kai, musamman idan sun fito daga babban malamin addini mai tasiri.

Ya jaddada cewa al’ummar Kano ba sa goyon bayan irin wadannan kalamai na rarrabuwar kai.

A cewarsa, shugabannin siyasa da na addini suna da babban nauyi na kare gaskiya, karfafa hadin kan al’umma da kuma samar da sulhu, maimakon yin kalaman da za su iya raunana tubalin hadin kan Najeriya.

Kwankwaso ya kuma ce zaben 2027 zai bai wa ’yan Najeriya damar saka wa shugabanci nagari da gagarumar kuri’a, tare da kin amincewa da rashin kyakkyawan aiki a rumfunan zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here