Home Labarai Mauludin Tijjani ya haɗu da cikas a Kano

Mauludin Tijjani ya haɗu da cikas a Kano

5
0

Gwamna Abba Ya ƙauracewa Halattar Mauludin Sheikh Ahmad Tijjani da aka gudanar a fadar sarki Aminu Ado dake gidan Nasarawa.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bai halarci Mauludin Sheikh Ahmad Tijjani (RA) da aka gudanar a Kofar Gidan Sarki da ke Nasarawa ba.

An dai shirya taron Mauludi da farko ne a Filin Kwallon Kafa na Sani Abacha, kafin daga baya aka sauya wurin zuwa Kofar Gidan Sarki wanda wasu ke cewa hakan ya faru ne sakamakon gwamnatin jihar kano ta hana taron sakamakon gayyatar Sarki Aminu Ado wanda gwamnatin bata tare dashi kamar yadda wasu ke zargi

Sauyin wurin ya haifar da ce-ce-ku-ce, musamman bayan Sheikh Ibrahim Dahiru Usman Bauchi ya gayyaci Aminu Ado Bayero, maimakon Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, wanda gwamnatin Kano ke marawa baya.

Wasu na ganin matakin na iya kasancewa yana da alaƙa da rashin amincewa da naɗin Sanusi II a matsayin Khalifan Tijjaniyya.

An zargi Shaikh Ibrahim Shiru Bauchi ne ke ƙara ruruta wutar wadda ke ƙara raba kan Tijjaniya a Nijeriya, Khalifa Sanusi na cikin waɗanda ke yiwa Tijjaniya hidima da ake ganin ya cancanci girmamawa a tsakanin mabiya da shugabannin ɗariƙar saɓanin a cigaba da jani’inja kan jagoranci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here