Home Labarai An kashe kwamandojin ISWAP 9 a samamen sama a dajin Sambisa

An kashe kwamandojin ISWAP 9 a samamen sama a dajin Sambisa

65
0

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta ce ta kashe aƙalla kwamandojin ƙungiyar ISWAP guda tara, ciki har da babban kwamanda Abu Khalid Al Muhajir, a wani samamen sama da ta kai a dajin Sambisa na Jihar Borno.

Kakakin rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an kai harin ne ranar Asabar bayan samun bayanan sirri kan zirga-zirgar ’yan ta’addan a yankin.

Ya ce an kuma jikkata wasu ’yan ta’addan, yayin da harin ya lalata wata maɓoyarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here