Home Labarai INEC Ta Ƙara Wa’adin Miƙa Sunayen ’Yan Takara ga Jam’iyyu

INEC Ta Ƙara Wa’adin Miƙa Sunayen ’Yan Takara ga Jam’iyyu

17
0

INEC Ta Ƙara Wa’adin Miƙa Sunayen ’Yan Takara ga Jam’iyyu

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da tsawaita wa’adin miƙa sunayen ’yan takarar shugaban ƙasa da na majalisun tarayya na zaɓen shekarar 2027 daga jam’iyyun siyasa.

Tun da farko, jadawalin da hukumar ta fitar ya nuna cewa wa’adin zai ƙare ne a ranar Asabar, 11 ga Yulin 2026, sai dai yanzu an ƙara wa’adin zuwa tsakar dare na ranar Talata, 14 ga Yulin 2026.

A cewar INEC, an ɗauki wannan mataki ne bayan ƙorafin da Majalisar Ba da Shawara ta Jam’iyyun Siyasa (IPAC) ta gabatar a madadin jam’iyyun da ba su samu damar loda sunaye da bayanan ’yan takararsu cikin lokacin da aka tsara ba.

Hukumar ta bayyana cewa tsawaita wa’adin ya nuna ƙudirinta na tabbatar da an bai wa kowa dama tare da bin tanade-tanaden doka.

INEC ta kuma yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da su yi amfani da wannan ƙarin lokaci wajen kammala loda dukkan bayanan ’yan takararsu kafin sabon wa’adin ya cika.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Kwamishinan Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, a ranar 12 ga Yulin 2026.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here