Home Labarai Hajjin 2027: Hukumar Alhazai ta Kano ta sanya wa’adin ƙarshe tare da...

Hajjin 2027: Hukumar Alhazai ta Kano ta sanya wa’adin ƙarshe tare da gargaɗi ga masu jinkirin biyan kuɗi sai bayan an rufe

23
0

Hajjin 2027: Hukumar Alhazai ta Kano ta sanya wa’adin ƙarshe tare da gargadi ga masu jinkirin biyan kuɗi sai bayan an rufe

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta sake jaddada cewa ranar 25 ga watan Satumban 2027 ita ce wa’adin karshe na biyan kudin ajiya da yin rajistar aikin Hajjin shekarar 2027, tare da gargadin cewa ba za a ba duk wani mai niyyar zuwa aikin Hajji gurbi ba bayan cikar wa’adin.

Shugaban hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim-Matawalle, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Sulaiman Dederi, ya fitar a ranar Laraba a Kano.

Sanarwar ta ce hukumar ta kayyade kudin ajiya na Hajjin 2027 zuwa Naira miliyan 8, tare da yin kira ga duk masu niyyar sauke farali da su kammala biyan kudinsu da kuma rajista kafin ranar da aka gindaya.

Darakta Janar din ya bayyana cewa sanya wa’adin na da matukar muhimmanci domin bai wa hukumar damar gudanar da shirye-shirye da tsare-tsaren aikin Hajjin 2027 cikin inganci.

Ya kuma sake tabbatar da kudurin hukumar na gudanar da aikin Hajji cikin tsari, gaskiya ba tare da wata matsala ba.

Haka zalika, Ibrahim-Matawalle ya shawarci duk masu niyyar zuwa aikin Hajji da su cika dukkan sharuddan rajista cikin wa’adin da aka kayyade domin kauce wa rasa damar sauke farali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here