Daga Aminu Abdullahi Gusau
Kwamitin Zaben Fidda Gwanin Sanata a karkashin Jam’iyyar APC a zamfara ta arewa, ya bayyana Sanata Tijjani Yahaya Kaura a matsayin wanda ya yi nasara, biyo bayan zaben da aka gudanar a ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba, 2026.
A cikin sanarwar hukuma da shugaban kwamitin, Sani Abdullahi, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa Kaura ne ya samu kuri’u mafi yawa a tsakanin ‘yan takara uku da suka fafata a zaben.
Sauran ‘yan takarar su ne Sanata Sahabi Ya’u Kaura da Sani Abdullahi Shinkafi.
Bisa ga sakamakon da kwamitin ya sanar, Sanata Tijjani Kaura ya samu kuri’u 16,758, yayin da Sahabi Ya’u ya samu kuri’u 1,565, shi kuma Shinkafi ya samu kuri’u 1,447.
A cikin sanarwar, shugaban kwamitin ya bayyana cewa Kaura ya cika dukkan sharuddan da kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC da ka’idojinta suka tanada; saboda haka, an ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma dan takarar jam’iyyar na kujerar Sanata a yankin Zamfara ta Arewa.
An fitar da sanarwar ne a madadin kwamitin, bayan da aka rawaito cewa shugaba da sakataren kwamitin ba su samu damar kasancewa a wurin ba, inda suka ba wani mamba na kwamitin umarnin ya sanar da sakamakon.
Sai dai, takardar sakamakon zaben ta nuna wasu sabani a alkaluman da aka bayar; inda aka ce jimillar masu zabe da aka yi wa rajista sun kai 23,257, yayin da aka tantance masu zabe 10,608, kuma aka samu kuri’u ingantattu guda 10,192.
Jimillar kuri’un da aka bai wa ‘yan takara ukun sun kai 19,770, adadin da ya zarce yawan kuri’u ingantattun da aka sanar. Wannan sabani ne da ke bukatar kwamitin zaben ya yi karin haske a kai.





