Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da aniyarta ta aiwatar da biyan ma’aikata alawus ɗin sufuri na naira 70,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi, domin rage musu raɗaɗin tsadar sufuri sakamakon cire tallafin man fetur. Gwamna Dakta Nasir Idris ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin ganawa da manema labarai a Abuja.
Gwamnan ya ce tuni ya kafa wani kwamiti ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati (Head of Service) domin tsara yadda za a aiwatar da biyan tallafin. Ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen inganta walwalar ma’aikata, musamman ganin yadda tsadar rayuwa ta rage ƙarfin kuɗin da suke samu.
Dakta Nasir Idris ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi na naira 75,000 ga ma’aikatan jihar, baya ga ƙarin naira 17,650 ga malamai. Ya ƙara da cewa gwamnati na gudanar da ayyukan gina gidaje 155 da wasu gidaje 250, tare da mayar da ma’aikatan wucin gadi sama da 1,700 cikakkun ma’aikata da kuma ɗaukar malamai 2,000 da wasu ma’aikatan lafiya.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba ta bin ma’aikata albashi, fansho ko garatuti, yana mai danganta hakan da ingantaccen kula da kuɗaɗen shiga da kuma ƙoƙarin toshe hanyoyin ɓarna. Ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya wajen aiwatar da manyan ayyukan hanyoyi a jihar.






