Gwamnatin Jihar Kano Ta Dakatar da kilisa ko Hawan Dowakai da Taron Durbar Har sai Baba tagani
Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da dukkan jerin gwanon Durbar da ayyukan hawan dawaki a cikin birnin Kano har sai wani lokaci.
Gwamnati ta ce matakin ya biyo bayan taron gaggawa na Majalisar Tsaro ta jihar, inda aka duba yanayin tsaro da ke tattare da shirye-shiryen gudanar da ayyukan.
Ta ce rahotannin tsaro sun nuna cewa dimbin magoya baya na shirin yin tururuwa, lamarin da ka iya haifar da arangama da karya doka da oda.
Gwamnatin ta umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da aiwatar da dokar, tare da yin kira ga mazauna Kano, sarakuna, ’yan siyasa da magoya bayansu da su zauna lafiya tare da bin umarnin.






