Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da shirin gaggawa na kwanaki 120 domin gyara matsalolin da suka addabi ɓangaren ilimi a jihar Zamfara.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ranar Litinin, bayan zaman Majalisar Zartarwa ta Jiha da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Gusau.
DCL Hausa ta ruwaito cewa a lokacin zaman Majalisar Zartarwa karo na 65, an amince da kafa kwamitin hadin gwiwa domin duba gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba da ke kusa da makarantu, tare da shirin korar su don tabbatar da tsaron wuraren karatu.
Haka kuma an amince da kudirin dokar ilimi guda daya da zai hada matakan daga ECCDE zuwa matakin jami’a, da kuma sauya ma’aikatan da ba na koyarwa ba zuwa wasu ma’aikatu ko kamfanoni.
A karshe, gwamnati ta ce za a kafa kwamitin musamman kan dokar ta-baci a fannin ilimi, tare da shigar da kungiyoyi kamar NUT, da hukumomin UNICEF, UBEC da sauran masu ruwa da tsaki domin aiwatar da gyare-gyare cikin gaggawa a fannin ilimi na Zamfara.






