Home Siyasa Gwamnan Kebbi ya aje mataimakinsa a takarar neman zango na biyu

Gwamnan Kebbi ya aje mataimakinsa a takarar neman zango na biyu

11
0


Gwamnan Kebbi Dakta INasir dris ya dauki Alhaji Ibrahim Muhammad Augie{Planner} matsayin mataimakinsa da za su yi takarar Gwamna a tare a kakar zabe ta 2027 in da zai nemi wa’adi na biyu.

Gwamnan ya aje mataimakinsa Sanata Umar Abubakar Tafida Argungu wanda suka nemi takarar ta Gwamna a wa’adi na farko in da suka samu nasara a tare.

Har yanzu Sanata Umar yana kan kujerarsa ta mataimakin Gwamna, sai dai takara ce da za a yi a karo ns biyu aka sauya shi da Planner.

Dakta Nasir ya ba da sanarwar zabin sabon mataimakin Gwamna a Lahadin na ya bayyana wanda ya zaba mai biyayya kuma wanda yake da goyon bayan talakawa da gogewa da sanin yakamata gwamnatinsa na bukatar goyon bayansa domin cika muradin mutanen jihar Kebbi. 

Ya ce zabar Ibrahim Augi hadaka ce da za ta mayar da hankali ga karfafa gwamnati da wanzar da zaman lafiya da kawo cigaba nan take mai dorewa a dukkan kanana hukumomin Kebbi 21.

Sauya mataimakin gwamna da aka yi ya zo da bazata a tsakanin siyasar jihar Kebbi ganin yanda suke tafiya tare, kuma ba wani bayani da aka fitar na gajiyawa daga mataimakin gwamnan, kawai dai ra’ayi ne ya sauya na shi gwamnan da kansa. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here