Nasarar Gwamnan Osun ta tunasar da mu cewa idan jama’a suka jajirce za a yi nasara ko da ba a shiga APC ba – Kwankwaso
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, murnar lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 15 ga Agusta, 2026.
Kwankwaso ya kuma yaba wa al’ummar jihar Osun bisa fitowa domin amfani da damar da dimokuradiyya ta ba su.
Ya kuma yaba wa Hukumar Zabe ta INEC, bisa yadda ta gudanar da zaben, tare da kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su ci gaba da tabbatar da sahihin zabe cikin lumana da gaskiya.






