Home Siyasa Zamfara: Jigo a APC ya yi murabus domin Tinubu ya kasa kawo...

Zamfara: Jigo a APC ya yi murabus domin Tinubu ya kasa kawo ƙarshen kashe-kashen da ake yi

15
0

Jigon APC ya yi murabus, ya ce Tinubu ya gaza kawo ƙarshen kashe-kashe

Wani jigo a jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, Hon. Muhammad Bello Yakubu Bakyasuwa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar, yana mai cewa ci gaba da hare-haren ’yan bindiga da kashe-kashen jama’a a jihar na daga cikin dalilan da suka sa ya ɗauki matakin.

Bakyasuwa, wanda ke cikin jam’iyyar a Dosara/Birnin Kaya Ward, Maradun LGA, ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da matsalar tsaro a Zamfara.

Ya ce rashin samun isasshen ci gaba wajen kawo ƙarshen ’yan bindiga da kashe-kashen fararen hula ya ƙara masa ƙwarin gwiwar barin APC.

Matakin ya zo ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke addabar Zamfara da wasu jihohin Arewa maso Yamma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here