Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar da martani ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, kan tambayarsa game da ci gaba da ciyo bashi duk da cire tallafin man fetur.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan sadarwar manufofi, Daniel Bwala, ya ce bashin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke karɓa ba domin almubazzaranci ba ne, sai dai domin zuba jari a muhimman fannoni na tattalin arziki.
Sarki Sanusi, wanda tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) ne, ya nuna damuwa a wata hira da News Central TV kan dalilin ci gaba da karɓar bashi bayan cire tallafin mai.






