Home Siyasa Duk wanda ya murde zaɓen 2027 za a aika shi lahira –...

Duk wanda ya murde zaɓen 2027 za a aika shi lahira – Omo-Agege

38
0

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ovie Omo-Agege, ya yi barazanar kashe duk wanda ya yi maguɗin zaɓen 2027 kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

Omo-Agege, wanda ke neman kujerar sanatan Delta ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), ya bayyana hakan ne yayin wani taron siyasa a mazabarsa.

“Duk wanda ya yi maguɗin zaɓe a ranar zaɓe, za mu kashe shi. Idan ba ka daraja rayuwarka ba, ka zo ka yi maguɗin zaɓe,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ba za su sake dogaro da kotu ba, yana mai cewa za su yi yaƙi da duk wanda ya yi ƙoƙarin ƙwace musu nasara.

Omo-Agege ya fice daga jam’iyyar APC a watan Mayun 2026, bayan ya shafe makonni yana tattaunawa da abokan siyasa da magoya bayansa, kafin ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar sanatan a zaɓen 2027.

Barazanar tasa ta zo ne mako guda bayan Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da gudanar da zaɓe cikin ’yanci, adalci da gaskiya a shekarar 2027.

Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya ce Tinubu ya kuma umarci jami’an tsaro su kasance masu tsaka-tsaki, tare da tabbatar da cewa dukkan ’yan Najeriya sun samu damar zaɓe ba tare da tsoratarwa ko nuna bambancin siyasa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here