Home Labarai Dole ne a yabawa Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto kan aiyukkan  raya karkara...

Dole ne a yabawa Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto kan aiyukkan  raya karkara da yake yi—-Bajare

9
0

Mai baiwa Gwamna shawara kan hanyoyin karkara Malami Muhammad Galadanchi wanda aka fi sani da Bajare ya yabawa Gwamnan Sakkwato kan ƙoƙarin da yake yi na  samar da hanyoyin karkara a faɗin jihar.

“Dole ne a yabawa Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto kan aiyukkan raya karkara da yake yi, a fili yake hakan zai bunƙasa taswirar gari da kuma bunƙasa tattalin arzikin al’umma.”

Galadanchi ya ce kammala hanyar Takatuku zuwa Ɗandamu wata nasara ce da gwamnatin Ahmad Aliyu ta samu a yunƙurinta na sauya fasalin gari, don ya shiga cikin jerin birane masu ƙayatarwa a Nijeriya, samar da aikin nan zai ƙaro cigaban noma, kasuwanci da sauran abubuwan more rayuwa.

Bajare ya ƙara da cewar wannan Gwamnati ta Dakta Ahmad Aliyu ta yi nasara wurin kawo cigaba a hanyoyin karkara hakan zai taimaka a samu tsayayyar taswira a faɗin jiha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here