Tinubu ya rusa ikirarin cewa EFCC na gudanar da aikinta ba tare da katsalandan ba – Atiku
Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ƙalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta umartar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ICPC ta saki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
Atiku ya ce idan har da gaske Shugaba Tinubu yana da ikon ba hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa umarnin yadda za su gudanar da ayyukansu, kamar yadda ya yi a kan Hukumar EFCC, to ya kamata ya kuma umarci ICPC ta saki El-Rufai.
Ya ƙara da cewa matakin da Tinubu ya ɗauka kan EFCC ya nuna cewa ikirarin da ake yi na cewa hukumar na gudanar da ayyukanta cikin ƴanci ba tare da tsoma bakin gwamnati ba, ba gaskiya ba ne.




