Home Labarai Dalilan Gwamnatin Kebbi na ƙirƙiro sabbin Masarautu biyu

Dalilan Gwamnatin Kebbi na ƙirƙiro sabbin Masarautu biyu

4
0

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da ƙirƙiro sababbin hakimai 2 a Ƙaramar Hukumar Argungu.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Ahmed Idris, ya fitar.

Ya ce, an naɗa Alhaji Abubakar Mohammad Mera a matsayin sabon Hakimin Yamman mai hedikwata a Gungu, Haka kuma, an ɗaga matsayin Gundumar Gwazange tare da naɗa Darikwai Muhammadu Ibrahim a matsayin Hakiminta.

Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bisa tanadin Dokar Ƙananan Hukumomi ta Jihar Kebbi ta shekarar 2008, wadda ta bai wa ƙananan hukumomi damar ƙirƙirar gundumomi da naɗa hakimansu.

Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na Jihar Kebbi, Alhaji Garba Umar Dutsinmari, ya buƙaci sabbin hakiman su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, riƙon amana, da jajircewa, yana mai tabbatar musu da goyon bayan gwamnatin jihar da ma’aikatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here