Matsalar Tsaro: Lokaci Ya Yi Da Jama'a Za Su Cire Tsoro ----Mashawarci Ga Gwaman Neja Kan Siyasa Da Tsare-Tsare

An kira ga al'ummar jihar Naija da su cigaba da baiwa jami'an tsaro hadin kai da goyon bayan wajen yaki da yan ta'adda a jihar. 

Matsalar Tsaro: Lokaci Ya Yi Da Jama'a Za Su Cire Tsoro ----Mashawarci Ga Gwaman Neja Kan Siyasa Da Tsare-Tsare

 

 

 

An kira ga al'ummar jihar Naija da su cigaba da baiwa jami'an tsaro hadin kai da goyon bayan wajen yaki da yan ta'adda a jihar. 

Mai baiwa gwamnan Naija shawara a harkokin siyasa da tsare-tsare, Honarabul Muhammad Nma Kolo ne yayi kiran littinin din makon nan a Minna lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da kokarin gwamnatin jihar na dakile hare-haren yan ta'adda a jihar.

Lokaci yayi da jama'a za su cire tsoro su rika tsegunta wa gwamnati duk abinda suke tsoron zai zama kutunguilar zaman lafiya, amma ba za mu cigaba da rayuwa cikin fargaba saboda son rai wasu mara son zaman lafiya suna mayar da mu baya ba.
Maigirma gwamna Abubakar Sani Bello a shirye yake a kowane lokaci wajen karfafa guiwar jami'an tsaro dan a murkushe 'yan ta'adda a jihar nan.
Da ya juya kan zargin da wasu ke yi na hannun gwamnati a zabukan shugabancin jam'iyya kuwa, yace jama'a ba su fahimci gwamna ba, ko a zaben kananan hukumomi da ya gabata a mazabar da gwamna ke zabe kansilan da PDP ta aje ne yaci zabe, gwamna bai amince a juya wannan zaben ba balle zaben jam'iyya da jama'ar jam'iyya ne suka zabi wanda suke bukatar yayi masu aiki.
Saboda kowani dan takarar mukami a jam'iyya na da damar cewar gwamnati ce ta turo shi, amma abinda na sani gwamna ya baiwa jama'ar APC zaben wanda suke ra'ayi, saboda ina karfafa guiwar yayan jam'iyyar APC su fito a duk lokacin da za a yi zaben shugabannin jam'iyya su zabi dan takarar da suke ra'ayi.
Yace ko halin da uwar jam'iyyar ta samu kan ta a shugabancin kasa da jahohi hakan na nuna cewar APC madauri daya ce da ta zama uwa daya uba daya wanda farin jini da kwarjinita yasa kowa ke sha'awar shiga cikinta dan a dama da shi.
Yanzu muna kan zaben shugabancin jam'iyya ne daga matakin mazabu, kananan hukumomi sannan jiha da kasa baki daya kafin babban zaben kasa mai zuwa, da ina da tabbacin siyasar da jam'iyyar APC ta ke shinfidawa a yanzu zai haifar mata da da mai ido a gaba.
Ina kara jawo hankalin al'ummar jihar Naija da su cigaba da baiwa gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello goyon baya, musamman kan ayyukan raya kasa da ta sanya a gaba, wanda zai zama alfanu ga al'ummar jihar nan.
 
Daga Babangida Bisallah, Minna.