Atiku,Tambuwal da Kwankwaso sun shiga sabon lissafi bayan baiwa Arewa shugaban PDP
Hakan ke nuna manyan 'yan takarar jam'iyar PDP daga Arewa kama da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da da tsohon shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki da Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso sun shiga sabon lissafi kan takararsu a jamíyar PDP domin da wuyar gaske a lokaci daya a zabi shugaban jam'iya da dan takarar shugaban kasa a yanki guda musamman a wannan halin da ake ciki na rabuwar kawuna a Nijeriya.
Masu son tsayawa takakarar shugaban kasa daga Arewa a PDP sun shiga sabon lissafi kan mika Kujerar shugan jam’iya a yankinsu.
A zaman da kwamitin karba-karba na jam’iyar PDP da Gwamnonin jam’iyar sun yi matsaya kan abaiwa yankin Arewa dammar fitar da shugaban jam’iya.
Shugaban Kwamitin kuma Gwamnan Jihar Enugu, Ifeanyi Ugwanyi, shi ne ya sanar da hakan ranar Alhamis bayan wani zama da suka yi a Abuja
Mista Ugwanyi ya ce Kwamitin Gudanarwar PDP na Kasa ya amince a yi musayar mukaman jam’iyyar tsakanin yankin Kudu da Arewa.
Sai dai ya bayyana cewa aikin da aka ba wa kwamitinsa bai shafi kujerar dan takarar shugaba kasa da mataimakinsa ba.
Sanarwar mayar da shugabancin jam’iyyar zuwa yankin Arewa ta biyo bayan taron da Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP ta yi ne a daren Alhamis.
A lokacin taron 9 daga cikin gwamnonin sun goyi bayan a mayar da shugabancin jam’iyyar zuwa yankin Arewa, 3 kuma suka zabi a mayar zuwa yankin Kudu a dan wani kwarya kwarya-kwaryar zabe da suka gudanar.
Hakan ke nuna manyan 'yan takarar jam'iyar PDP daga Arewa kama da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da da tsohon shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki da Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso sun shiga sabon lissafi kan takararsu a jamíyar PDP domin da wuyar gaske a lokaci daya a zabi shugaban jam'iya da dan takarar shugaban kasa a yanki guda musamman a wannan halin da ake ciki na rabuwar kawuna a Nijeriya.
Managarciya na hasashen za a kai takarar shugaban kasa ne a yankin kudu idan lokacin tsayar da dan takara ya yi duk da an nuna ba a tabo wannan batun a wurin zaman ba.
managarciya