Home Siyasa Daga 2027 ba zan sake tsayawa takarar shugaban ƙasa ba—-Atiku

Daga 2027 ba zan sake tsayawa takarar shugaban ƙasa ba—-Atiku

2
0

Atiku Abubakar ya ce zaɓen 2027 ne zai kasance na ƙarshe da zai fafata Amatsayin ɗan takarar shugaban ƙasa

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 shi ne na ƙarshe da zai shiga a siyasarsa.

Atiku, wanda ya fara fafatawa neman shugabancin ƙasa tun daga shekarar 1992, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na tashar Arise Television a ranar Laraba.

Ya ce wannan shawara tasa ta nuna cewa lokaci ya yi da zai kammala yunkurinsa na neman shugabancin ƙasa bayan shekaru da dama yana gwagwarmaya a fagen siyasa.

Wannan furuci nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan shirye-shiryen zaɓen 2027 da kuma makomar manyan ‘yan siyasar ƙasar.

Shin wannan ne ƙarshen tafiyar Atiku a takarar shugaban ƙasa? Lokaci ne zai bayar da amsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here