Home Siyasa Da’ace Tinubu Ya So APC Ta Ci zaɓen Osun da ni zai...

Da’ace Tinubu Ya So APC Ta Ci zaɓen Osun da ni zai tura don lashe zaɓen—Wike

9
0

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce da ace Shugaba Bola Tinubu ya ƙuduri aniyar ganin APC ta lashe zaɓen Osun, da ya je jihar domin taimaka wa jam’iyyar, kuma da sun yi nasara.

Wike ya bayyana cewa: “Da Shugaban ƙasa ya so lashe zaɓen Osun ko ta halin kaka, da na je can, kuma da mun yi nasara.

INEC ta bayyana Gwamna Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Wike ya kuma ce zaɓen 2027 zai kasance mafi sauƙi ga Tinubu fiye da na 2023, saboda a cewarsa, ‘yan adawa sun yi rauni kuma ba su da ƙarfin da za su iya kalubalantar Shugaban ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here