Home Siyasa Kamfen Shugaban ƙasa a Nijeriya zai soma daga Ranar Laraba

Kamfen Shugaban ƙasa a Nijeriya zai soma daga Ranar Laraba

8
0

Yayin da wa’adin fara yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Ƙasa a zaɓen 2027 zai fara gobe, Laraba 19 ga Agustan 2026, manyan jam’iyyun siyasa na ci gaba da tuntubar juna domin kammala tsarin kwamitocin yaƙin neman zaɓensu.

Rahotanni sun ce jam’iyyun APC, ADC da NDC har yanzu ba su kammala kafa kwamitocin yaƙin neman zaɓensu ba, sakamakon wasu rikice-rikicen cikin gida, da kuma tattaunawar rabon mukamai bisa la’akari da yankuna, baya ga wasu shari’o’in da ke gaban kotuna.

A jam’iyyar APC, ana ci gaba da nazarin sunayen waɗanda za su jagoranci kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu. Daga cikin sunayen da ake ambata akwai tsohon Gwamnan Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura; Gwamnan Imo, Hope Uzodinma; da tsohon Gwamnan Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari.

A ɓangaren jam’iyyar ADC kuwa, ana duba tsohon Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, da tsohon Gwamnan Cross River, Liyel Imoke, a matsayin waɗanda za su iya jagorantar kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar.

Hakan na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙoƙarin kammala shirye-shiryensu gabanin fara yaƙin neman zaɓen babban zaɓen ƙasar na 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here