Home Siyasa Ci bayan ilmi da yanki na ke fama da shi yana damuna—Alhaji...

Ci bayan ilmi da yanki na ke fama da shi yana damuna—Alhaji Umar Ajiya 

7
0
0-4160x3120-0-0-{}-0-12#

Dan takarar Sanata a yankin Sakkwato ta Gabas a jam’iyyar APC Alhaji Umar Ajiyan Isa bayan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar a zaɓen 2027, ya yi jawabi ga ɗimbin mutanensa don neman goyon bayan su.

Alhaji Umar Ajiya ya bayyana damuwarsa yanda mutanensa musamman matasa maza da mata ba su zuwa makaranta domin an rufe makarantun kan  matsalar tsaro, in da mafiyawan makarantu a yankin ‘yan gudun hijira ne ke zaune  a ciki.

“Za mu yi ƙoƙari mu haɗa kai tsakanin gwamnatin jiha da tarayya da jami’an tsaro, da taimakon kowa da kowa da yarda Allah za mu yi  abin da ya dace a samar da tsaro, yana cikin abin da ke ciwa mutane tuwo a ƙwarya ba Sakkwato kaɗai ba jihohi da dama, akwai buƙatar baiwa jami’an tsaro goyon baya mu yi aiki tare da gwamnatoci mu haɗa hannu domin ta yi mana maganin matsalar.

“Bayan matsalar tsaro harkar ilmi ta ci baya a yankimu, na uku babu kasuwanci, waɗan nan su ne alƙiblarmu za mu yi aiki da gwamnatin jiha da tarayya don samowa mutanenmu maslaha, duk Jumu’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake ganewa kan haka  kafin mu shiga gwamnati mun san matsalar da mutanenmu ke ciki, sannan muna yin daidai gwargwadon abin da muke iyawa don mu ba gwamnati ba ne, ba mu iya abin da za ta yi shi ne dole mu goya mata baya, mu ga cewa abin ya yiwu, abin da ake buqata a haxa kai a yi aiki tare.

“An bani damar ne domin naje na qwatowa mutane na haqqinsu, a duk san da na zo Sakkwato ina son na je qauyenmu amma ina saboda abubuwan da suka taso kusan shekara 20 yanzu tun suna qanana ba a yi maganinsu ba, har suka fi qarfin jama’a, da ikon Allah za mu samo zaman lafiya ga mutanenmu domin su yi noma da kasuwanci.

“Yaranmu ba su zuwa makaranta domin babu makarantun sun koma wurin zaman ‘yan gudun hijira abin na damuna yanda yankina ya koma baya, muna son gwamnatin tarayya ta ba mu wasu haqqinmu yanda ake yi wasu yankuna, kamar hanyar mota da asibitoci da sauransu, ana fakewa da ba mu da tsaro shi ne dalilin rashin yi, abaiwa mutanenmu aikin sai su yi,” Kalaman Umar Ajiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here