Home Manyan Labaru Bayan kashe mutane  15 ce-ce-ku ce ya barke a tsakanin mutanen Zamfara

Bayan kashe mutane  15 ce-ce-ku ce ya barke a tsakanin mutanen Zamfara

17
0

‘Yan ta’adda Sun Kashe Mutane  15 a garin Sado dake qaramar Hukumar Talata Mafara a ranar Jumu’a data gabata.

 Bayan kammala sallar Janazar mutanen ne da ‘yan bindiga suka shigo garin suka kashe ba tare da wani laifi ba.

Shugaban qaramar hukumar Talatar Mafara Alhaji Yahaya Abubakar Yari ya yi kira ga qaramin ministan tsaro Alhaji Bello Matawalle da ya dubi mutanen Zamfara ya kawo masu dauki domin mutanen da aka kashe a jihar abin ya yi yawa.

“Babu ruwana da siyasa wallahi, amma abin da ya faru yau dole a sanar duniya cewa qarya ce ake yi, na fito fili ne na yi  magana ba a voye ba, kai ne waqilin Zamfara a majalisar zartarwa ta qasa, kai ne ijiyarmu, a yankinka a maqwabciyar qaamar hukumarka wannan abun ya faru, mai girma minsta ka dubi talakawa nan da idon Rahama, na kalli wani bidiyon ka a kwanan baya ka ce an samu sauqin tsaro a Zamfara, abin da idona ya gani a yanzu haka gani a wannan qauyen na Tungar Vore, zan karva tambaya a gaban Allah kaima idan ka tsaya kan wannan maganar za ka amsa tambaya a gaban Allah, wata biyu ko uku  da suka wuce ka yi alqawalin za ka kawo sojojii 1000 su kare mutane,” ya furta haka yana kuka.

Xan takarar Sanata Zamfara ta Gabas Dakta Mika’ilu Barau a bayanin da ya rubuta kafarsa ta facebook ya nuna minisatn tsaro akwai waxanda suke gabansa wurin samar da tsaro a jiha.

“Gwamna da Sanata sun fi minista haqqi a kan tsaro ga duk wanda ya fahimci tsarin Nijeriya na yau.”

Sadiya Bello Barade Kodineta ta GEEP a Zaamfara ta miqa saqon ta’aziyarta ga waxanda suka rasu tare da yin addu’ar Allah ya kawo qarshen wannan lamarin.

Barade ba ta xaura laifi kan kowa ba a lokacin da fitar da bayani sai dai ta yi addu’a kan lamarin tsaron Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here