Naɗa mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan tsaron cikin gida Adeyinka Famadewa ya haifar da cece ku ce kan tsarin tsaron na shugaban ƙasa Bola Tinubu a gwamnatinsa.
Shugaba Tinubu a yanzu baya Nijeriya ya ba da sanarwar a Litinin a wani daftari da sakataren gwamnatin tarayya ya sanyawa hannu.
Wasu na ganin muƙamin ya yi daidai wasu na ganin an samar da muƙamin kan siyasa domin a ragewa mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaron ƙasa Malam Nuhu Ribadu ƙarfin iko.






