Home Labarai Ba wanda ake cilastawa ya shiga musulunci—Sarkin Musulmi

Ba wanda ake cilastawa ya shiga musulunci—Sarkin Musulmi

22
0

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa babu wanda ya kamata a tilasta masa shiga addinin Musulunci.

Sarkin ya kuma bukaci Musulmi da su mutunta ’yanci da hakkokin mabiyan sauran addinai domin tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummar Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a wajen babban taron NSCIA da aka gudanar a Masallacin Kasa da ke Abuja.

Sarkin Musulmin ya ce Musulunci bai amince da tilasta wa mutum shiga addini ba, yana mai cewa mutane da dama suna shiga Musulunci ne bisa radin kansu.

“Ba mu da niyyar tilasta wa kowa ya shiga Musulunci. Amma mun ga yadda mutane da dama suke shiga Musulunci da son ransu, domin Allah Madaukakin Sarki ya ce babu tilastawa a cikin addini,” in ji shi.

A nasa bangaren, Babban Sakatare na NSCIA, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bukaci iyayen Musulmi da su tabbatar da cewa ’ya’yansu sun samu ilimin addinin Musulunci tare da ilimin zamani.

Oloyede ya kuma yi kira da a kara samun wakilcin Musulmi a kafafen yada labarai da kuma wuraren aiki, yana mai cewa ya kamata shugabannin Musulmi su tabbatar da cewa kwararrun ’yan al’umma ana ba su damar rike muhimman mukamai.

Ya ce akwai jihohin da Musulmi suka fi yawa da ke fama da koma baya wajen ilimi, yana mai jaddada cewa ya kamata al’ummar yanzu su samu ingantaccen ilimin addini da na zamani.

Haka kuma, Oloyede ya yi tambaya kan ci gaba da rawar da gwamnati ke takawa wajen shirya aikin Hajji, inda ya ce aikin gwamnati ya kamata ya fi karkata wajen saukaka wa alhazai gudanar da ibadar.

Ya kuma yi gargadi kan bai wa mutanen da ba su da karfin yin tafiya tallafin aikin Hajji.

Kalaman Sarkin Musulmin sun zo ne makonni kadan bayan da ya yi kira ga Musulmi da Kiristoci a Najeriya da su daina zagin juna, yana mai cewa hakuri da juna a harkar addini na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here